Harin da ɗan bindiga ya kai tare da kashe mutane 59 a wani otel da ke Las Ɓegas na ƙasar Amurka, ga alama zai bayar da damar zaunawa domin yi wa dokar mallakar makamai a ƙasar garambawul.
Bayanai na nuni da cewa, yanzu haka jam’iyyar Republican da kuma masu kamfanonin ƙera bindigogi na gaf da cimma matsaya kan wannan batu, lamarin da zai bawa majalisar dokokin damar tattaunawa kan yadda za a yi wa tsarin bawa jama’a damar mallakar makamai gyaran fuska.
Bayanai na nuni da cewa irin bindigogin da ɗan bindigar ya yi amfani da su wajen kai wannan hari, bindigogi ne da ka ƙara ingantawa a baya-baya nan, lamarin da kuma ke ƙara jefa fargaba a cikin zukatan Amurkawa.