Gwamnatin tarayya ta sanar a ranar Asabar cewa, Amurka ta cire duk wasu kudaden tallafi na biza ga ‘yan Nijeriya da ke neman biza zuwa kasar wanda ya fara daga ranar 3 ga Disamba.
Da yake bayyana hakan a karshen mako, Ministan Ma’aikatar Harkokin Wajen ya ce ci gaban ya biyo bayan cire takardar izinin biza da ta wuce gona da iri, da kuma sarrafa kudaden da ake bai wa ‘yan asalin Amurka da ke neman bizar Nijeriya. Idan za a iya tunawa, gwamnatin Donald Trump a shekarar 2019 ta sanya kudin karba don duk wasu takardun neman izinin da za a ba ‘yan Nijeriya da basu amince da su ba.
An cajin kudin ban da kudin neman biza don masu neman izinin da aka ba su biza. Tsarin kudin rarar da aka biya daga Dala 80 zuwa Dala 303 ya dogara da nau’in biza, wanda ya fara aiki daga 29 ga watan Agustan bara.
Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce kudaden rarar da aka yi na mayar da martani ne ga tattaunawar da a samu nasara da Najeriya ba don daidaita kudaden da take karba wa Amurkawan da suka nema.
Ta yi ikirarin cewa jimillar kudin da dan kasar Amurka zai samu bizar zuwa Nijeriya ya fi yawan kudin da dan Nijeriya zai samu kwatankwacin bizar zuwa Amurka.
Ofishin Jakadancin ya nace cewa an ba da kudin rarar ne don kawar da bambancin farashin kamar yadda dokokin Amurka suka bukata.
Da yake bayani kan dokar cire tallafin kudin bizar a cikin wata sanarwa, mai magana da yawun MFA, Ferdinand Nwonye, ya ce, “Ma’aikatar Harkokin Wajen na son sanar da cewa Gwamnatin Amurka ta cire duk wasu kudaden tallafin biza ga‘ yan Nijeriya da ke neman biza zuwa Amurka.
“Kyakkyawan ci gaban ya yi daidai da cire tallafin bisa mai yawa, sarrafawa da kuma biyan kudade don samun sukunin biyan kudin ‘yan asalin Amurka da ke neman bizar Nijeriya da Gwamnatin Nijeriya ke yi.
“Don haka Gwamnatin Amurka ta cire kudaden tallagin ga ‘yan Nijeriya tun daga ranar 3 ga Disamba, 2020.” Sanarwar mai taken, ‘Sabuntawa Kan Cire kudin Tallafin biza ga ‘yan Nijeriya da Gwamnatin Amurka ta yi.’
Da Dimi-diminsa: Buhari Ya Sauya Shugabannin Rundunonin Tsaro
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da murabus din shugabannin...