Amurka Ta Kakaba Wa Turkiya Takunkumi

Gwamnatin Amurka ta saka wa wasu ma’aikatun gwamnati da wasu manyan jami’an gwamnatin Turkiya takunkumi a wani martani kan hare-haren da Turkiyar ke kai wa Arewacin Siriya.

Shugaba Donald Trump ya kuma kira takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan inda ya nemi a tsagaita wuta ba da bata lokaci ba.

Sojojin Siriya dai sun isa wasu yankuna da ke arewa maso gabashin kasar, kuma wannan na iya haifar da wani fito-na-fito tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da na Turkiya.

Shigar sojojin Siriya wannan yankin ya biyo bayan wata yarjejeniya da aka kulla ne tsakanin dakarun Kurdawa da na Siriyan bayan da Amurka ta juwa wa Kurdawan baya.

Turkiya ta ce tana kai wadannan hare-haren ne saboda ta mayar da ‘yan Siriya kusan miliyan biyu can bayan ta samar da abin da ta kira “yankin tsaro”, wanda zai kai fadin kilomita 30 cikin Siriya daga kan iyakarta.

A halin yanzu akwai miliyoyin ‘yan Siriya da ke gudun hijira a Turkiya.

Amma yawancin ‘yan gudun hijiran ba Kurdawa ba ne, kuma wasu na ganin wannan matakin na Turkiya na iya haifar da wata matsalar – wato Kurdawan na iya rasa muhallansu da garuruwansu gaba daya.

 

Exit mobile version