Amurka Ta Tsaurara Matakan Ba ‘Yan Gudun Hijira Kan Takardar Biza

President Donald Trump pauses during a prison reform roundtable in the Roosevelt Room of the Washington, Thursday, Jan. 11, 2018. (AP Photo/Carolyn Kaster)

Gwamnatin Shugaba Trump na tsaurara matakan bai wa ‘yan gudun hijira damar shiga Amurka, ta hanyar binciken kwakwaf ga masu neman shigowa daga kasashe 11 da ake dauka a matsayin masu tsananin hadari.

Jami’ai sun ki bayyana sunayen kasashen masu tsananin hadarin, lokacin da suka kira manema labarai domin bayyana wannan canji, amma an yi ta bayyana kasashen a rahotanni. Kasashen sun hada da Masar, da Iran, da Iraki, da Libiya, da Mali, da Koriya ta Arewa, da Somaliya, da Sudan ta Kudu da Sudan, da Siriya da kuma Yamal.

Wani jami’i ya ce banbanci daya da za a gani shi ne yi wa mutanen da suka fito daga kasashen tambayoyi masu zurfi, sabbin matakan da aka dauka za su shafi kasashen da ke cikin jerin sunayen, kuma zai iya haifar da jinkiri ga wasu masu shiga kasar.

Ana kyautata tsammanin yawancin sauye-sauyen da aka yi za su fara aiki zuwa karshen watan Maris, a cewar wani jami’i.

 

Exit mobile version