CRI Hausa" />

Amurka Tana Da ’Yancin Yada Labarai, Gaskiya Ce Ko Karya?

A ranar 2 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da kayyade yawan ma’aikatan Sin ga hukumomin reshen kafofin watsa labarai na kasar Sin guda biyar dake kasar Amurka.

Amurka ta ce, ta dauki wannan mataki bisa ka’idar adalci. Amma, kasar Sin ba ta taba kayyade yawan ma’aikata ga hukumomin kasar Amurka dake kasar ta ba. Yanzu haka dai akwai hukumomin kafofin watsa labarai guda 29 na kasar Amurka dake kasar Sin, amma ana da hukumomin kafofin watsa labarai guda 9 kacal na kasar Sin dake kasar Amurka. Shin ko akwai adalci a tsakanin su?
Haka zalika kuma, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, wasu kafofin watsa labarai na kasar Amurka, sun keta ka’idar zaman ‘yan jaridu, har sun fitar da labarai na jabu, domin bata sunan kasar Sin, lamarin da ya bata ran al’ummomin kasa da kasa. Martanin da kasar Sin ta mayarwa wasu kafofin watsa labaran kasashen waje, ta dace ka’idoji da dokokin kasar, kuma, ta kasance tsadar da ya kamata su biya, dangane da mugun aikin da suka yi wajen bata sunan kasar Sin.
Amma kasar Amurka, ta sanya takunkumi kan kafofin watsa labarai guda biyar na kasar Sin, bisa hujjar cewa, wadannan kafofin watsa labarai guda biyar suna karkashin mallakar gwamnatin kasar Sin. A hakika dai, tana korar ‘yan jaridu na Sin daga kasarta. Lamarin da ya bayyana karyar da kasar Amurka ta kitsa kan ‘yancin yada labarai, kuma kasar Amurka tana yunkurin nuna kiyayya kan manufofin siyasar kasar Sin.
Kasashen duniya suna da bambanci, kuma ba wanda zai hana kasar Sin ci gaba da raya tattalin arzikinta. Kiyayyar da kasar Amurka ta nunawa kasar Sin ba ta da amfani, kuma ba ta dace da halin da ake ciki a yanzu ba, kawai dai za ta kawo matsala ne ga mu’amalar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, yayin da take bata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A karshe dai, matakin zai haddasa asara ga Amurka ita kanta. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version