Koriya ta Arewa, ta ce Amurka za ta dandana kudarta, sakamakon jagorantar zartar da matakin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, na kakaba mata sabbin takunkuman karya tattalin arziki.
Zalika manyan ami’an Koriya ta Arewan sun ce a kowane lokaci suna iya sake gwajin wani makamin Nukilyar, bayan nasarar da suka samu dari-bisa-dari a gwajin da suka yi a ranar 3 ga Satumba na makamin nukiliyar mai dauke da sinadarin Hydrogen.
Amurka na son kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya haramta wa cinikayyar danyen mai da Koriya ta Arewa, da kuma sanya wa shugaban Korea ta Arewan Kim Jong Un takunkumin tafiye-tafiye.
A farkon makon da muke, shugaba Kim Jong-Un ya gudanar da wani gagarumin bikin cin abinci domin karrrama masana kimiyar kasar, wadanda suka taimaka wa kasar kera makamin nukiliyar da aka gwada makon jiya.
Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce shugaban ya gudanar da bikin ne tare da manyan hafsoshin sojin kasar, inda aka yi raye-raye da daukar hoto tare da shugaban.
Hotan da aka nuna na bikin na dauke da shugaba Jong-Un tare da wasu masana kimiyar kasar guda biyu Ri Hong Sop, na Cibiyar kera nukiliyar kasar da kuma Hong Sung Mu, mataimakin Daraktan Jam’iyyar da ke mulkin kasar.