CRI Hausa">

Amurka Za Ta Girbi Zambar Da Mr. Pompeo Ya Shuka Bisa Ga Shirinsa Na “Tsaftace Yanar Gizo”

Kwanan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya yi ta rura wutar shirinsa na wai “tsaftace yanar gizo”, wato “Clean Network” a Turance, a wani kokari na kawar da kayayyaki, da hidimomin da kasar Sin ta samar daga wasu fannoni biyar, ciki har da sadarwa, da manhaja da sauransu. A sa’i daya kuma, fadar White House ta sanar da haramta manhajojin sada zumunta na kasar Sin, da suka hada da Tik Tok, da Wechat da sauransu. Matakan da aka dauka a sakamakon babban zaben da ba da jimawa ba za a gudanar a kasar, tare kuma da neman dakile ci gaban kasar ta Sin.

Sai dai matakan za su kuma lahanta moriyar al’ummar kasar Amurka, wadanda suke amfani da manhajojin. A zamanin da muke ciki, ko fasahar sadarwa ta 5G, ko kuma kafofin sada zumunta ta Tik Tok da kuma Wechat, baya ga kasancewarsu hidimomin da aka samar, sun kuma kasance dandali na musayar bayanai a tsakanin al’umma, da nishadantarwa, da samar da damammakin kasuwanci. A sabo da haka ne, bayan sanarwar ’yan siyasar White House game da haramta yin amfani da Tik Tok, sai wasu sanannun masu fada a ji a yanar gizo, suka aika wa shugabannin Amurka wasika, don bayyana rashin jin dadinsu, kuma a ganinsu, hakan zai janyo hasarar wani muhimmin dandali na yin fashin baki ga al’ummar Amurka.
A hannu daya kuma, yadda gwamnatin Amurka ke yunkurin korar kamfanonin kasar Sin, zai girgiza niyyar kasashen duniya ta zuba jarinsu a Amurka, tare da gaggauta janye kamfanoninsu daga kasar. Yadda ’yan siyasar Amurka irinsu Pompeo suke fakewa da shirin “tsaftace yanar gizo” a yau, don dakile kamfanonin kasar Sin, zai sa su kori kamfanonin sauran kasashe a gobe.
Ban da haka, idan an yi hangen nesa, yadda kasar Amurka ke dakile abokiyar takararta ba bisa ka’ida ba, da kuma keta dokokin kasuwanci, ba shakka zai rage karfinta ta fannin tattalin arziki.
A daidai lokacin da ’yan siyasar Amurka ke aiwatar da shirinsu na yin babakere, a ranar 8 ga wata, a hukumance gwamnatin kasar Sin, ta gabatar da shawarar tsaron bayanai ga kasa da kasa, inda ta ba da shawarwari guda takwas, dangane da nuna kyamar yin amfani da fasahohin sadarwa wajen lalata manyan ababen more rayuwa na wasu kasashe, ko kuma satar muhimman bayanai da sauransu, shawarwarin da suka bayyana niyyar kasar Sin na kiyaye tsaron bayanai na kasa da kasa. (Lubabatu Lei)

Exit mobile version