Sakataren Bitalmalin, Amurka Stebe Mnuchin, ya fada a shekaran jiya Juma’a cewa yana kan bakarsa na halartan babban taron zuba jari a kasar Saudiy Arabi a karshen wannan wata, duk da tarin shaidar da ke nuna an kashe dan jaridar Saudiyar a ofishin jakadancin Saudi Arabia a Istanbul a Turkiya.
Mnunchin ya fada wa telabijin CNBC cewa yana ci gaba da shirinsa na halartan taron. Ya ce, idan wani abu ya biyo bayan haka, ko kuma an samu wata sakiya, zai yi nazari akai, amma dai yana kan batun zuwa taron.
Wasu manyan bankuna a dandalin hada-hadar kasuwancin duniya na Wall Street, za su halarci wannan babban taron kasuwanci a birnin Riyadh, duk da cewar wasu manyan kamfanonin yada labarai da manyan ‘yan kasuwa sun janye daga halartan taron, kana suka daina huldan kasuwanci da yankin Gabas ta Tsakiya.
Hamshakin dan kasuwar Birtaniyan nan Richard Branson ya fada a Juma’ar nan cewa zai dakatar da tattaunawarsa a kan taron zuba jarin na Saudi Arabia a kamfaninsa na Birgin Groups.
Wasu manyan ‘yan kasuwa kamar Stebe Case daya daga cikin masu kamfanin kasuwancin yanar gizo AOL, da mai kamfanin sufuri na Uber Dara Khosrowshahi da Robert Bakish mai kamfanin Biacom, duk sun ce ba za su halarcin taron na Riyadh ba.