Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin Trump ta kasar Amurka tana tsara wasu tsauraran matakan kayyade samar wa kasar Sin sassan na’urorin hada laturoni na semiconductor, da kara matsin lamba ga kasashen kawacenta, tare da bukatarsu da su tsaurara dabaibayi a kan sha’anin samar da fasahar matattarar bayanai ta microchip ga kasar Sin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau 25 ga wannan wata cewa, kasar Sin ta riga ta sanar da matsayinta ga kasar Amurka kan batun kayyade samar da sassan na’urorin laturoni na semiconductor ga kasar Sin sau da dama.
Ya ce, Amurka ta siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya da kimiyya da fasaha, da maida batun a matsayin barazana ga tsaron kasa, da kara hana fitar da mattarar bayanai ta microchip ga kasar Sin, da sa kaimi wajen ganin sauran kasashe sun hana bunkasa sha’anin samar da sassan na’urorin laturoni na semiconductor ga kasar Sin, kana ya ce wannan mummunan aikin na Amurka zai hana bunkasar sha’anin samar da sassan na’urorin laturoni na semiconductor a duk duniya, kuma a karshe dai za ta illata kanta. (Zainab Zhang)