Bello Hamza" />

Amurka Za Ta Janye Daga Yarjejeniyar Makamai Da Ta Kulla Da Rasha

Amurka ta aikewa da Rasha sakon gargadi, kan cewa za ta janye daga matsayar da aka cimma ta takaita kera madashin makaman nukiliya da na masu linzami.
A jiya Juma’a shugaba Trump ya bayyana cewa, Amurka za ta janye daga wannan matsaya, wacce aka kwashe gomman shekaru da rattaba hannun akanta, inda ta zargi hukumomin Kremlin da take matsayar.
A cewar Trump, Rasha ta jima tana kera makamai masu linzami da aka haramta, wadanda ke zama barazana ga kawayen Amurka da dakarunta da ke kasashen waje.
Sai dai, hukumomin Rashan sun yi maza sun musanta ikrarin na Amurka, suna masu cewa, Amurka na neman hanyar ne kawai, da za ta fadada rumbun makamanta masu linzami.

Exit mobile version