Amurka Za Ta Lashe Amanta Game Da Karin Harajin Rashin Adalci Da Ta Bugawa Kasar Sin
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Za Ta Lashe Amanta Game Da Karin Harajin Rashin Adalci Da Ta Bugawa Kasar Sin

byCGTN Hausa
1 year ago
Amurka

A ranar Talata 14 ga watan nan ne gwamnatin Amurka, ta sanar da buga karin haraji kan wasu hajojin dake shiga kasar daga kasar Sin, matakin da ya gamu da nuna rashin jin dadi, da adawa daga al’ummar duniya. 

Amurka ta rika siyasantar da batun ciniki, wanda hakan ya keta hurumin hada-hadar cinikayyar sassan biyu, kuma zai illata bunkasuwar harkoki masu alaka, daga karshe dai Amurka za ta lashe amanta tare da gamu da babbar illa.

  • Daga Karshe, Biden Ya Zamanto Irinsu Trump
  • Shugabannin Sin Da Rasha Sun Tattauna Da Juna

Hajojin da gwamnatin Amurka ta dorawa matsin lamba a wannan karo sun shafi musamman na fannin amfani da makamashi mai tsabta. Sakamakon haka muna iya ganin cewa, zargin da wasu manyan jami’an Amurka suka yi, cewar wai yawan hajoji masu aiki da makamashi mai tsabta da Sin ke samarwa sun wuce misali, hujja ce kawai ta neman buga karin haraji.

To ko mene ne dalili? Manazarta na ganin cewa, a wani bangare, Amurka ta gaza samun karfin takara a wannan bangare, shi ya sa ’yan siyasar ta suke yunkurin dakile hada-hadar Sin mai fifiko bisa manufar kariyar cinikayya.

A wani bangare na daban kuwa, matakin ya kasance wani wasan kwaikwayo na siyasa, duba da cewa, za a gudanar da babban zaben Amurka a bana. Amma, a halin yanzu ana fuskantar hauhawar farashi, da gibin kasafin kudi mai tsanani da dai sauran kalubaloli, don haka dora laifi kan wasu, mataki ne da ’yan siyasar kasar Amurka suka dade suna aiwatarwa.

Sana’ar samar da hajoji masu aiki da makamashi mai tsabta ta kasar Sin, ba ma kawai ta samarwa duniya isassun hajoji ba ne, har ma ta sassauta hauhawar farashinsu a duniya, kuma ta taka rawar gani wajen tinkarar sauyin yanayi, da karkata zuwa hanyar samun bunkasuwa ba tare da bata muhalli ba. Don haka dai yunkurin Amurka na dakile kasar Sin ba zai hana ci gabanta ba, sai dai kawai ya fayyace rashin hangen nesa, da kasancewa mai keta ka’idar duniya. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Kaddamar Da Taron Koli Na LAS Karo Na 33

Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Kaddamar Da Taron Koli Na LAS Karo Na 33

LABARAI MASU NASABA

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version