“Amurka Za Ta Taimakawa Nijeriya Bankado Masu Daukar Nauyin Boko Haram”

Daga Sulaiman Ibrahim,

Amurka ta bayyana shirinta na taimakawa Nijeriya wajen bankado masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.

Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Leonard ce ta bayyana hakan ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Yayin da aka tambayi jakadiyar ko Amurka a shirye take ta taimakawa Nijeriya gano masu daukar nauyin ta’addanci a kasar.

Sai ta amsa da cewa ana ci gaba da tattaunawa kan lamarin.

Leonard ta ce, “Wannan wani abu ne da muke matukar son hada gwiwa da Nijeriya akan lamarin.

“Na yi akalla tattaunawa uku a cikin watanni biyu da suka gabata kan wannan batun.

Exit mobile version