An Amince Da 27,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashi  

Majalisar gudanawar ta kasa ta amince da Naira 27,000 a matsayin mafi karancin albashi, ministan ayyuka da kwadago, Dakta Chris Ngige ne ya bayyana hakan yau Talata, bayan da majalisar ta yi wani zama a garin Abuja.

Amma dai ita gwamnatin tarayya za ta biya ma’aikatan Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi, kamar yadda kungiyoyin kwadago suka bukaci gwamnatin, wannan sanarwar ta biyo bayan zaman da majalisar gudanarwar ta yi, wanda shugaban kasa Buhari ya jagoranta a fadar gwamnatin tarayya.

Ministan ya bayyana cewa nan da awanni 24 za su mika kudurin ga majalisun tarayya don sanya shi cikin dokokin kasa, ministan ya ce ma’aikatan gwamnatin tarayya za su dinga daukar 30,000 a matsayin mafi karancin albashi, inda ma’aikatan jihohi kuma zasu dinga daukar 27,000, haka ma’aikatan masana’antu masu zaman kansu ma.

Ministan ya ce an amince ne da shawarar da kwamitin ‘yan uku wanda Ama Pepple ta jagoranta, kwamitin ya sanya 30,000 a matsayin mafi karancin albashi, amma gwamnatoccin jihohi sun dage a Naira 24,000, an shafe awanni uku ana zaman majalisar gudanarwan, cikin wadanda suka halarci zaman akwai tsohon shugaban kasa Obasanjo, Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan, Tsofaffin manyan Alkalan Nijeriya ma su halarta.

 

A Biyo mu don samun cikakkun labarai…

Exit mobile version