Connect with us

TATTALIN ARZIKI

An Amince Da Dage Karin Kudin Lantarki Bisa Sharadi

Published

on

Kamfanonin masu rarraba wutar lantarki a Nijeriya (DisCos) sun amince da dage shirinsu na kara kudin wutar lantarki a farkon watan Yuli, sakamakon wata ganawa da suka yi da shuwagabannin Majalisar Dokoki ta Nijeriya.

DisCos sun ruwaito cewa, sun amince da dage karin kudin wutar lantarki har zuwa farkon wata ukun shekara mai zuwa, yayin da shugabannin majalisa su ka sha alwashin za su tattauna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan wannan lamari.

DisCos sun bayyana cewa, idan shirin karin kudin ya kai har zuwa shekara mai zuwa, to gwamnati za ta ci gaba da cike mabambantan gibin da su ke samu wajen gudanar da rarraba wutar lantarki.

An dai samu cikakken bayanin ganawan ne ta bakin jami’in yada labarain na shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, mai suna Ola Awoniyi. A cewar wannan bayanin, Mista Lawa da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da manya-manyen shugabannin majalisun guda biyu da shugaban hukumar da ke kula da wutar lantarki da kamfanoni masu rarraba wutar lantarki a cikin kasar nan suka amince ga DisCos ta su dage karin wutar lantarkin. A cikin wadanda suka halacci wannan taro sun hada da shuwagabannin kwamitun wutar lantarki na majalisar dattawa da na majalisar wakilai.

‘Yan majalisun sun bayyana cewa, a yanzu ba lokacin da ya dace a kara kudin wutar lantarki ba ne, duk da karin tsadar da ake samu wajen samar da wutar lantarki, akwai bukatar a janyo masu zuba jari a bangaren wutar lantarki. Da yaka ne muke kira ga DisCos da su janye kudirinsu na shirin karin kudin wutar lantarki, duk da suna bukatar yin karin kudin wutar lantarkin.

“A cikin yarjejeniyar da muka cimma da ku, ba za ku kara kudin wutar lantarki ba a ranar 1 ga watan Yuli. Shugaban majalisar wakilai da kuma ni kaina za mu dauki matakin ganawa da shugaban kasa a kan wannan lamari.

“Mun amince a nan a kan babu wani tsarin na kara kudin wutar lantarki a wannan lokaci, sannan akwai bukatar aiwatar da wani tsari a kan lamarin. Tsakanin yanzu har zuwa farkon wata ukun shekara mai zuwa, za su gudanar da aiki tare domin tabbatar da ganin mun dakile duk wani ynkuri na karin kudin wutar lantarki,” in ji Lawal.

Ya bayyana cewa, shirin karin kudin wutar lantarkin ya shafi ayyukan ‘yan majalisa, saboda yana daya daga cikin aikin gwamnati a matsayinsu na wakilan jama’a.

“Na sani a wannan shekara da kuma shekarar da ta gabata, an kashe kudade a bangaren wutar lantarki wanda ya kai na naira biliyan 600 wajen farfado da wannan fanni. An samu matsaloli da dama a cikin rayuwar ‘yan Nijeriya da kuma Duniya gaba daya sakamakon matsalolin da cutar Korona ta haddasa, ko da ya ke akwai matsaloli da dama ga mutanenmu wajen biyan kudin wutar lantarki.

“Harkokin kasuwanci da dama sun dogara ne da wannan fanni wajen gudanar da su, domin jayo masu zuba jari a wannan fanni, ya kamata mu bi wasu hanyoyin da suka dace, sannan idan za mu yanke hukunci mu yi kokarin duba lokacin da ya fi dacewa,” in ji shi.

Da ya ke gabatar da jawabi, shugaban majalisar wakilai, Mista Gbajabiamila ya bayyana cewa, majalisa da kuma DisCos ba sa hanya daya wajen nuna yawan kudin wutar lantarki.

“Dukkan shirye-shiryen ko manufofin da gwamnati take kokarin aiwatarwa da shi ne a zahirance, sannan ba za su taba dawowa ba idan ta aiwatar da su lokacin da bai dace ba. Ina tunanin dukkanmun amince da wannan lamari.

“A yanzu halin da ake cikin ba lokaci ba ne na yin karin wani abu ba ne. Ya kamata a ijiye wutar lantarki a gefe na wani lokaci. A yanzu lokaci ne na farfado da kudaden shiga, mun rage farashin man fetur. A ganina wannan ba lokacin da ya dace a yi karin kudin wutar lantarki a Nijeriya.

“Idan aka yi karin wutar lantarki a wannan lokaci zai shafi gwamnatin shugaba Buhari, haka kuma muma zai shafe mu. Dukkan mu mun dogara ne da mutane, dole shugaban kasa da makarraban gwamnati su yi wa mutane abin da ya dace,” in ji shi.

A cikin mahalarta taron akwai wakilan hukumar da ke kula da wutar lantarki a Nijeriya da kamfanin da ke rarraba wutar lantarki reshen Jihar Kano da kamfanin da ke rarraba wutar lantarki a Ikeja da kamfanin da ke rarraba wutar lantarki a Jihar Kaduna da kuma kamfanin da ke rarraba wutar lantarki a Eko.

A cikin watan Junairu ne, hukumar da ke kula da wutar lantarki a Nijeriya ta bayyana cewa, za ta kara kudin wutar lantarki a duk fadin kasar nan daga ranar 1 ga watan Afrilu. Amma an daye wannan shirn na kara kudin wutar lantarki sakamakon tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ganin yadda Duniya ke cikin durkushewar tattalin arziki sakamakon barkewar cutar Korona.

Mafi yawancin ‘yan Nijeriya sun yi Allah wadai da wannan karin, sun bayyana cewa, karin ba zai kawo wani canji a cikin harkokin samar da wutar lantarki ba. Sun kuma bayyana cewa, za a samu canji ne kawai idan masu amfani da wutar lantarki suna biyan ainihin kudin wutar lantarki, sannan a kyale ‘yan kasuwa su zuba kudade masu yawa domin farfado da wannan fannin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: