Daga Rabiu Ali Indabawa,
Wani ma’aikacin gidan gona mai suna Paulo, an ruwaito ya samu raunuka bayan da aka azabtar da shi da gawayi mai zafi saboda satar kwai hudu a kasar Zimbabwe. A cewar rahoton iHarare, wani mai suna Leon Koza ya kona kafafun dan shekara 34 mai suna Personal Paulo da garwashin wuta mai zafi, wanda a sanadiyyar hakan ya samu munananraunuka, inda rahotanni suka tabbatar da cewa shi surukin mai gonar Plumstead Farm ne inda yake aiki a ciki.
Da yake bayanin yadda lamarin ya faru, ma’aikacin manomin, Paulo ya bayyana cewa Koza wanda ya gano cewa ya saci kwai ya daure shi da wani karfe, ya yi masa duka da sanda har sai da kafafunsa suka kumbura, daga baya ya dauki gawayi mai zafi ya fara kone masa kafafun yana mai fada masa cewa sata ba kyau.
Ma’aikacin gonar ya kuma bayyana cewa an kai masa harin ne a ranar 6 ga Fabrairu kuma ya nemi likita ne kawai a ranar 26 saboda Koza ya yi masa barazanar zai sa a kama shi tare da korarsa daga gonar.
An kuma gano cewa Paulo ya sami damar zuwa neman magani ne kawai bayan ‘yar uwarsa, wacce ta ziyarce shi, ta gano cewa dan uwan nata yana da raunuka a kafafunsa wanda ke zub da jini kuma ya kasa tafiya.
An gabatar da rahoto a Ofishin ‘yan sanda na Banket wanda ya kai ga cafke Koza, wanda tun lokacin da ya bayyana a gaban kotu kuma aka ba da izinin tsare shi a kan beli kyauta zuwa ranar 19 ga Maris 2021.