CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

An Ba Da Amsa Kan Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Kasar Sin Ta Samu Amincewa Sosai

by CRI Hausa
March 13, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
An Ba Da Amsa Kan Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Kasar Sin Ta Samu Amincewa Sosai
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A ‘yan shekarun da suka gabata, jerin binciken ra’ayin jama’a da cibiyoyin kasa da kasa suka yi, sun nuna cewa, kason Sinawa dake goyon bayan gwamnatinsu ya kai matsayin farko a duniya. To, ko mene ne dalilin? Sakwannin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayar a yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 11 ga wata, bayan rufe manyan tarukan biyu, wato taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa (CPPCC), da na majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC), sun bude wata taga ga kasashen duniya don kara fahimtar wannan dalili.

Daga cikin sakonnin akwai, “Samar da aikin yi tubali ne na zaman rayuwar jama’a, kuma tushe ne na samun ci gaba”, “Kamata ya yi gwamnati ta zuba kudi a fannin kyautata zaman rayuwar jama’a, musamman ma ta fuskokin ba da ilmin tilas da hidimar jinya” da dai sauransu……

Wadannan batutuwan sun shafi rayuwar kowa da kowa. Harkokin jama’a na da muhimmanci gaya, kamar dai yadda sakon da aka fitar a bayyane a taron manema labarum yake,–“Babban burin neman ci gaban kasar Sin shi ne, bai wa Sinawa damar zaman rayuwa mai kyau.”

A wannan rana kuma, hukumar kolin kasar dake tsara dokoki ta zartas da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 14, da burin da ake fatan cimmawa nan da shekara ta 2035. An kuma gabatar da muhimman muradu 20 da za a cimma a shekaru biyar masu zuwa, inda guda bakwai suka shafi zaman rayuwar jama’a, adadin da ya wuce kashi daya cikin uku.

Daga sanya rayuwar mutane da lafiyarsu a gaba a yayin da ake fuskantar matsalar kiwon lafiyar jama’a, zuwa sanya batun samar da aikin yi a gaban komai lokacin da ake kokarin farfado da tattalin arziki, har zuwa bada muhimmanci ga inganta rayuwar jama’a a yayin da aka tsara shirin raya kasa na nan gaba, a ko da yaushe, gwamnatin Sin na martaba manufar bada muhimmanci ga harkokin jama’a yayin da take gudanar da ayyukanta, wato tana kokarin yin duk abubuwan da jama’ar kasar ke bukata. Wannan ne kuma babban dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta samu amincewa sosai na tsawon lokaci. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

SendShareTweetShare
Previous Post

An Yi Wa Gwamnan Bauchi Allurar Rigakafin Korona

Next Post

Kyautata Tsarin Zaben Hong Kong Zai Ba Da Kariya Matuka Ga Tsarin Demokuradiyyar Yankin

RelatedPosts

Yaushe Za’a Yi Wa Al’ummomi Marasa Rinjaye Adalci A Amurka?

Yaushe Za’a Yi Wa Al’ummomi Marasa Rinjaye Adalci A Amurka?

by CRI Hausa
11 hours ago
0

Daga CRI Hausa Bayan da aka shafe tsawon makonni uku...

Don Me Kasar Sin Ta Gabatarwa Duniya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”?

Don Me Kasar Sin Ta Gabatarwa Duniya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”?

by CRI Hausa
12 hours ago
0

Daga CRI Hausa Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar...

Kasar Sin Jigon Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Kasar Sin Jigon Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

by CRI Hausa
23 hours ago
0

Daga Ibrahim Yaya A wannan mako ne aka bude taron...

Next Post
Kyautata Tsarin Zaben Hong Kong Zai Ba Da Kariya Matuka Ga Tsarin Demokuradiyyar Yankin

Kyautata Tsarin Zaben Hong Kong Zai Ba Da Kariya Matuka Ga Tsarin Demokuradiyyar Yankin

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version