Connect with us

WASANNI

An Ba Wa Partey Shawarar Koma Wa Arsenal

Published

on

Tsohon dan wasan tawagar kasar Ghana, Samuel Attah, ya shawarci dan wasa Thomas Partey akan cewa yayi iya yinsa domin ganin ya koma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a kakar wasa mai zuwa idan an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

A watan daya gabata wasu rahotanni suka bayyana cewa  dan wasan ya amince da komawa kungiyar Arsenal din bayan ya amince da irin albashin da zai dinga karba a karkashin mai koyarwa Mikel Arteta.

A satin daya gabata ne daman aka bayyana cewa dan wasa Thomas Partey, yafi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal duk da irin neman da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German take masa.

Dan wasan dan shekara 26 a duniya dai ya bayyana kansa a kungiyar kwallon kafar ta Atletico Madrid wanda hakan ne yaja hankalin kociyan kungiyar ta Arsenal yake nemansa domin ya karawa kungiyar tasa karfi a tsakiyar fili.

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu nasarar jan hankalin dan wasan ne bayan doguwar tattaunawa da wakilin dan wasan wanda yaje ya zauna da wakilan Arsenal din a Landan.

Tun a shekarar data gabata ne Arsenal ta fara bibiyar dan wasan dan asalin kasar Ghana wanda yana daga cikin ‘yan wasan da suka kasance zakaran gwajin dafi a kungiyar Atletcio Madrid musamman a karkashin mai koyarwa Diego Simeone.

“Yakamata ace yanzu Partey yana buga kwallon kafa a kasar Ingila saboda kwarewarsa da kuma yadda nake ganin idan ya koma Arsenal zai taimakawa kungiyar sannan kuma tauraruwarsa zata daga sosai” in ji Attah

Ya ci gaba da cewa “Arsenal babbar kungiya ce wadda kowanne dan wasa zaiso ace zai koma cikinta saboda irin tarihin da take dashi bama a kasar Ingila ba har a duniya gaba daya saboda haka ina ganin lokaci yayi da zaiyi amfani da wannan damar domin ya cika burinsa na buga babbar kungiya”

Dan wasa Partey dai yana da farashin fam miliyan 44 kuma tuni kociyan kungiyar, Mikel Arteta ya bawa shugabannin kungiyar kwarin guiwar cewar idan har suka sayi dan wasan kwalliya zata biya kudin sabulu.

Kungiyar kwallon kafa ta PSG dai ta dade tana bibiyar dan wasan da ake ganin shine yake buga irin salon tsohon dan wasan Chelsea da Real Madrid, Michael Essien, sai dai tuni Partey ya karkatar da tunaninsa zuwa kungiyar Arsenal.

Sakamakon matsalar tattalin arziki da kungiyoyi  suka shiga saboda annobar cutar Korona, anyi zaton PSG zata samu damar doke Arsenal wajen sace zuciyar dan wasan musamman idan tayi masa tayin albashi mai tsoka sai dai Arsenal ma a wannan lokacin ta kokarta.

Tuni dai kungiyar Atletico Madrid ta bayyana cewa a shirye take data sayar da dan wasan idan har Arsenal ta amince za ta iya biyan abinda take bukata saboda kungiyar tana bukatar kudi musamman a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

Advertisement

labarai