Connect with us

WASANNI

An Ba Wa PSG Gasar Lig One Ta Kasar Faransa

Published

on

An bayyana kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain a matsayin wadda ta lashe gasar rukuni-rukuni ta kasar Faransa ta shekara ta 2019 zuwa 2020, bayan da gwamnatin kasar ke tsoron yada cutar korona idan aka koma buga wasannin na bana.

Gwamnatin Faransa ce ta ce ba za a koma wasanni ba cikin sauri har sai watan Satumba don gudun yada annobar, dalilin da ya sa ta soke wasannin shekarar nan kuma hukumar kwallon kafar kasar ta yanke shawarar bawa PSG kofin.

PSG ce kan gaba a teburi da tazarar maki 12 da kwantan wasa daya, a lokacin da aka dakatar da gasar ranar 13 ga watan Maris don gudun yada cutar korona sai kungiyar kwallon kafa ta Lille a mataki na biyu.

A farkon makon nan Firai Ministan Faransa, Edouard Philippe ya sanar da soke kakar wasanni ta 2019 zuwa 2020 inda yace gwamnatin kasar ba zata sake bari a sake komawa baya ba a kokarin da kasar take yi na yaki da cutar.

Hukumar kwallon kafar Faransa ta so a ci gaba da wasannin shekarar nan ranar 17 ga watan Yuni, domin karkare kakar bana sai dai kungiyoyin Amiens da ta Toulouse sun fado daga gasar Ligue 1, bayan da suke karshen teburi.

An bayyana Lorient a matsayin wadda ta lashe gasar Ligue 2 saboda kungiyar tana mataki na daya a kan teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Lens kan a dakatar da wasannin bana saboda Koronan.

Babban jami’in gasar French League, Didier Kuillot ya ce daga nan zuwa 25 ga watan Mayu za su sanar da hukumar kwallon kafar Turai, Uefa, kungiyoyin da za su wakilce ta a gasar Champions da Europa League a badi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: