An Bai Wa Dalibai Horo Kan Yaki Da Cin Zarafin Jinsi A Yanar Gizo

Kimanin dalibai 24 ne suka ci gajiyar samun horo na musamman daga cibiyar bunkasa fasaha tare da kawo cigaba (CITAD) a jihar Jigawa.

Shugaban gudanar da ayyuka na musamman a cibiyar Kwamred Ali Sabo ne ya bayyana haka a yayin taron horaswar wadda a ka gudanar a ofishin cibiyar dake birnin Dutse.

Haka kuma ya bayyana cewa, daliban wadanda‎ su ka fito daga Jami’ar tarayya da ke Dutse (FUD) da kuma Kwalejin kimiyya da fasaha da ke Dutse sun ci moriyar wannan shiri kyauta wadda cibiyar ta CITAD tare da wata kungiya da ke Bauchi.

Kwamred Ali Sabo ya ce, duba ‎da yadda amfani da yanar gizo ya zama wajibi a rayuwarmu ta yau da kullum kuma da yadda ake cin zarafin jinsi ta wannan hanya, hakan ya sanya wannan cibiya dukufa wajen wayar da kan matasa kan yadda zasu yi amfani dashi ta yadda ya dace ba tareda cin zarafin wani ko wata ba.

Haka kuma horan zai basu damar sanin ‘yancinsu gamida matakan da zasu iya dauka domin gujewa afkuwar makamantan irin wadannan abubuwa na cin zarafi ko muzantawa a yanar gizo ta hanyar wata kafar‎ sadarwa.

Daga karshe ya yi kira ga matasan da su yi amfani da wannan horo da a ka ba su wajen koya wa sauran ‘yan uwansu matasa ire-iren wadannan dabaru domin a gudu tare a tsira tare.

Exit mobile version