Umar A Hunkuyi" />

An Bankado Haramtattun Matatun Mai A Gezawa

Sashen kula da albarkatun man fetur da ke Kano, ya kulle wasu wurare biyu a bisa zargin su da hannu a kan tatso wani abu da ake kyautata zaton man fetur ne.
Matatun man guda biyu na haramun da aka gano a wasu garuruwa guda biyu da suke a wajen garin na Kano, a karamar hukumar Gezawa, suke ta Jihar.
An gano haramtattun matatun man guda biyu ne a sakamakon wani binciken sirri da sashen na kula da albarkatun man fetur a tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na farin kaya da ke shiyyar ta Kano suka yi.
Babban shugaban sashen na Kano da Jigawa, Alhaji Musa Zarumi Tambawal, wanda shi ne ya jagoranci tawagar jami’an sashen wajen kulle haramtattun matatun man ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da aka tatso a haramtattun matatun man biyu.

Exit mobile version