Daga Rabiu Ali Indabawa,
An gano wani da ake zargi da garkuwar, satar mutane da kuma yin tsafi a cikin wani rami a yankin Sari-Iganmu da ke Legas, a kan babbar hanyar Orile-Badagry. Sassan jiki da kayan hade-hade kamar kayan makaranta, karama safa, damara da sauransu, an ruwaito cewa an same su a cikin wani kogo. Ramin yana gaban Makarantar Sakandaren Araromi, wata makaranta dake tsakiyar unguwa a cikin jama’a.
Rahotanni na nuni da cewa mutum biyun da aka kama a cikin ramin sun kone kurmus yayin da aka ce an mika wasu biyu zuwa ofishin ‘yan sanda na Orile-Iganmu. Wasu majiyoyi daga yankin, sun ba da haske kan yadda aka gano wurin, suna cewa wata yarinya mai sayar da burodi tana ta shawagi a kan babbar hanyar da misalin karfe 5 na yamma a ranar Lahadi lokacin da ta hango wasu maza suna yawo da zarto a cikin ramin.
An ce yarinyar ce ta yi kururuwar da ta sanya matasa suka shiga wurin.
An gano cewa mazaunan sun ci gaba da bincike a rami a ranar kuma sun sake kama wasu mutum biyu da ake zargi – wani saurayi da dattijo – yayin da aka gano sassan jikin mutum a wurin.
“Sun banka wa matashin wuta suka ceci wannan dattijo, wanda suke ganin zai ita fadar abin da ke faruwa a wurin. An mik shi ga jami’an hukumar kula da makwabta ta jihar Legas. Sun samu Naira 17,00 a dunkule a wurinsa daga nan suka tafi da shi ofishin ‘yan sanda. An samu sassan jikin da kuma kawunan mutane a cikin ramin. ” In ji wata majiya.