An Baro Shiri Tun Rani Game Da Shigo Da Abinci Ba Tare Da Biyan Haraji Ba
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Baro Shiri Tun Rani Game Da Shigo Da Abinci Ba Tare Da Biyan Haraji Ba

byAbubakar Abba
1 year ago
Abinci

A kwanakin baya ne, gwamnatin tarayya ta shelanta cewa; ta amince da shigo da abinci cikin kasar nan daga kasashen ketare, har na tsawon kwanaki 150; ba tare da biyan ko sisin kwabo a matsayin haraji ba.

Har ila yau, kayan abincin da gwamnatin ta amince a shigo da su din sun hada da; Masara, Shinkafa, Alkama da sauran makamantansu, wanda ta ce; ta dauki wannan mataki ne, domin dakile hauhawar farashin kayan abinci a dukkanin fadin wannan kasa baki-daya, kamar yadda Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya shaida wa manema labarai a Abuja.

  • Nijeriya Da Amurka Sun Jaddada Kudurin Karfafa Kasuwanci A Tsakaninsu
  • Gwamnatin Kano Ta Sayi Taki Tirela 180 Domin Bunkasa Noma A Jihar

Sai dai kuma, wakilinmu ya ji ta bakin wasu masu ruwa da tsaki wadanda kuma manoma ne a kan wannan batu, inda akasarinsu suka nuna cewa, gwamnatin ta riga ta baro shiri tun rani.

Haka zalika, daya daga cikinsu; Alhaji Adamu Makarfi, Shugaban Manoman Masara na Arewa Maso Yamma; a hirarsa da LEADERSHIP Hausa ya bayyana cewa, wannan mataki; ko kadan ba zai haifar wa da Nijeriya da mai Ido ba, domin kuwa kamata ya yi bayan an zabi Shugaba Tinubu a matsayin shugaban kasa; ya ayyana dokar ta baci a fannin aikin noma, musamman ta fuskar magance kalubalen rashin tsaro, duba da yadda ake kashe manoma a Arewacin wannan kasa babu ji babu gani. Haka zalika, kyautuwa ya yi a ce ya wanzar da kudurinsa na magance kalubalen rashin tsaron, ta yadda ‘yan kasa za su gani a kasa, ba kawai kuma sai a siyasantar da fannin ba; da sunan daukar matakin shigo da abinci ba tare da biyan haraji ba, domin duk kasar da aka ce babu abinci, ko shakka babu za ta kasance cikin babbar fitina da halin dardar.

Makarfi ya ci gaba da cewa, akasari tun kafin zuwan wannan gwamnati, ana sayar wa da manoma takin zamani ne a kurarren lokaci; sannan kuma da matukar tsada duba da yadda kusan a bana, aka sayar da takin zamanin a kan kusan farashin Naira 40,000 duk buhu guda, wanda hakan ke jawo musu dimbin asara, musamman ma kananan manoma.

Kazalika, ya yi nuni da cewa; kamata ya yi a rika sayar musu da takin zamanin a kan lokaci, sannan kuma gwamnati ta sayar musu da shi cikin rahusa, wanda hakan zai ba su kwarin gwaiwar noma amfani mai yawa; wanda zai iya wadatar da wannan kasa.

Ita ma wata manomiya, Hajiya Aisha Abubakar a hirarta da wakilinmu ta bayyana cewa, matakin gwamnatin tarayyar ba zai wadatar wajen karya farashin abinci ba, domin kuwa Nijeriya na bukatar dimbin tantan na abinci; kafin a iya wadata kasar da abinci, musamman duba da karuwar yawan al’ummar kasar a halin yanzu.

Ta kara da cewa, rashin sama wa manoman ingantacce Irin noma, hakan na jawo musu tabka asara da kuma rashin mayar da hankali a bangaren gwamnati, musamman gwamnatin tarayya na samar da kayan aikin noma na zamani; wanda ko shakka babu ke yi wa fannin matukar illa tare da samar da koma baya.

Shi kuwa wani babban manomi, a bangare guda kuma tsohon shugaban kunkiyar masu kiwon kajin gidan gona, reshen Jihar Kaduna; Alhaji Musa Bala a zantawarsa da LEADERSHIP Hausa ya yi nuni da cewa, matakin gwamnatin tarayyar; tamkar riga Malam Masallaci ne, domin kuwa ko da an shigo da abincin,  akwai wasu baragurbin da za su saye baki-daya; su kuma rika sayar wa da al’umma, musamman talakawa a kan farashi mai matukar tsada.

Bala ya kara da cewa, kamata ya yi yadda Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci  a wannan fanni, sai kuma ya sa a dawo da tsari irin na da; wato na kafa hukumar kayyade farashin kayayyaki, musamman kayan abinci; amma wannan mataki na shigo da kayan abincin cikin wannan kasa, musamman domin magance hauhawar farashin kayan; ba zai taba yin wani tasiri ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
Next Post
Tallafin Man Da Nijeriya Ke Biya Yanzu Ya Zarce Nb700 Duk Wata – IPMAN

Tallafin Man Da Nijeriya Ke Biya Yanzu Ya Zarce Nb700 Duk Wata – IPMAN

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version