An Bayar Da Alluran Rigakafin COVID-19 Sama Da Biliyan 1.5 A Sin

Daga CRI Hausa

Ya zuwa jiya Alhamis, an baiwa al’umma alluran rigakafin cutar COVID-19 sama da biliyan 1.5 a kasar Sin.

Hukumar kiwon lafiyar kasar wadda ta bayyana hakan, ta ce ya zuwa ranar 8 ga watan nan na Yuli, adadin nau’o’in rigakafin COVID-19 na kasar Sin 22 ne suka shiga matakin yin gwaji kan mutane. Kuma tuni aka baiwa wasu 4 izinin shiga kasuwa, yayin da wasu 3 suka samu izinin yin amfani da su a mataki na gaggawa a cikin kasar.

Da farko dai an kaddamar da gangamin yiwa al’ummar Sinawa da shekarun haihuwar su suka haura 18 ne rigakafin cutar ta COVID-19, inda ya zuwa tsakiyar watan nan na Yuli kuma, wasu lardunan kasar, da yankuna, da birane suka ayyana shirin su na kaddamar da yiwa yara, dake tsakanin shekaru 12 zuwa 17 rigakafin na COVID-19. (Saminu)

Exit mobile version