Connect with us

KASUWANCI

An Bayyana Dalilin Da Ya Sa Tashar Jirgin Saman Inugu Ba Zai Yi Aiki Da Dare Ba

Published

on

Filin  jirgin sama na Akanu Ibiam na kasa da kasa dake Enugu, ykna daya daga cikin filayen jiragen sama na Najeriya da ba’basu kulawar data kamata ba ganin ana kolle filin da karfe 6:00 na yammar ko wacce rana saboda rashin fitilu akan hanyar da jerage me sauna da tashi.

Hakan ya janyowa filin rashin daraja da kuma samarwa da Gwamnatin Tarayya kudin shiga kamar yadda filayen jirage na Kano, Fatakwal, Abuja Legas da sauran manyan filayen dake kasar suke samarwa.

Zirayar zuwa gani da ido da takagar Hukumar NCAA ta yi a  satin da ya gabata ta biyo bayan koken da kungiyar gamnonin yankin Kudu Maso Yamma suka yi ne na kiran Gwamnatin Tarayya ta kawowa filin dauki, musamman fitilolin  hanyar da jiragen suke sauka  lalace  Gwamna Dabid Umahi na jihar Ebonyi ya bayyana jin dadinsu akan daukin da akan filin jirgin da Gwamnatin take kanyi a yanzu, sai dai sun ja hankali akan yadda fitilolin dake kan hanyar da jaragen suke sauka ta lalace matuka da inda ake ajiye jaragen, inda suka yi kira ga ministan Sururin Jirage ya ziyarci filin don ganewa idonsa.

Idan ba’a manta ba FAAN a watan Janairun 2018 ta kulle filin na wucin gadi don a gudanar da yin gyara  akan hanyar da jiragen suke tashi da sauka yadda aka fadada shi har manyan jiragen kamar Boeing 777 da kuma na A380 zasu iya sauka.

Amma a ziyara da wakilin my ya kai a kwanan baya,ta nuna cewar, wasu sauran bangarorin hanyar ta sauka da rashin sunada matsala, inda suke hanawa jiragen karfin sauka.

A cewar Darakta Janar na  NCAA Kafgin  Mukhtar Usman, wannan ba zai haifar da wata matsala ba wajen tashi ko sauka ba dole ne a rufe hanyar kamar yadda aka rufe ta Nnamdi Azikiwe dake  Abuja a lokacin da ake yin gyaran hanyar sauka da tashin jaragen. Ya ce, a jirgi muka sauka a nan akwai abubuwa da dama da za a yi a filin don a inganta shi an shirya za a yi irin gyran da aka yiwa na Abuja.

Daya daga cikin kalubalen shine yadda jiragen basa iya sauka da dare saboda rashin na’urar sauka da kuma fitilolin sauka akan hanyar sa.

Manajin Darakta na riko na   FAAN, Injiniya Salisu Daura ya ce ana bukatar nisan da ya kai na tsawon kilo mitar daya na sanya fitilolin.Daura  ya kara da cewa, dole sai anyi Rusau na wasu gine-ginen domin a yanzu anada kilomita  420 ne kacal, Inda ya yi nuni da cewar sauka lafiya ita ce tafi babban mahimmanci ya kuma yi kira ga gwamatin jihar ta Ebonyi itama ta Kawo dauki.
Advertisement

labarai