Idris Aliyu Daudawa" />

An Bayyana Muhimmancin Duba Idanu A Kalla Sau Daya A Shekara

Wani kwararre a banagern kula da lafiyar al’umma wanda yake asibitin Ido a asbitin Ido na wanda yake aiki a Ultimate Eye Clinic, Lagos, Dokta Emeka Iwuala ya bayyana bukatar da ake da ita, na mutane su rika zuwa aka- akai ana duba lafiyar idanun su.
A wata ganawar da yayi da wakilin mu, Iwuala ya bayyana cewar wasu daga cikin cututtukan idanu kamar su glaucoma, basu da wasu alamu, za kuma su fito a Idon ba tare da shi mutumin ya sani ba.
“ Dalilin shne muna fadin cewar mutane su rika duba lafiyar idanun su, a kalla sau daya a shekara, shi ne watakila ana iya samun wasu matsaloli, a cikin idanun, dalilin da yasa muke cewar mutane su rika zuwa ana duba idanun su, a kalla sau daya a shekara shine, watakila ana iya samun matsalol a cikin idanun, wadanda wanda ke fama da cutar ba zai iya sani ko ganewa ba.
“Ya ci gaba da cewar ‘Mutum yana iya tsammanin ganin shi yana da kyau, amma kuwa mai yiyuwa akwai wata marsalar da kai baka sani ba, wannan shi yasa ma mun bayar da shawarar cewa, koda mutum yana gani sosai babu wata matsala, ya kamata ya je gwada ma shi ko duba ma shi idanun shi a kalla sau daya a shekara, kamar dai yadda Iwuala ya bayyana “.
Y kuma kara jaddada cewar yadda ake barin idanu suna kallon Komfuta ko kuma waya zuwa wani lokaci maio tsawo, sai iya kasancewa babbar matsala ga idanu, saboda suna iya samar da matsala ta causeomputer wanda wata matsala ce wadda ke kawo cikas wajen gani sosai.
“ Wasu mutane suna iya kasancewa duk tsawon rana kan waya da kuam Komfuta, saboda wannan yana iya sanadiyar zasu rika jin cewar akwai wani abinda yake damun shi a idanun shi, ya yin da wasu kuma suna iya samun ciwon kai.
“ Abinda muka ba mutane shawara musamman wadanda suka daukar dogon lokaci suna amgani da Komfuta shine, ya kamata su rika amfani da wata na’ura wadda zata rage hasken da yake shiga idanun su daga Komfuta.,”
Shi kwararren ma’aikacin lafiyar IdanuThe Optometrist, har ila yau ya ba mutane wadanda suke amgani da Komfuta zuwa wani lokaci mai tsawo, kullun shawarar su ri1a amfani da 20:20:20 wanda wannan yana nuna yin aiki na minti 20, a kan Komfuta, mutum kum kuma ya dan barta na minti 20 ba dakika 20. Har ila yau ya ba mutane shawarar kada su yi awa wadda ta wuce uku suna amgani da Komfuta sabofa kada su sa idanun su cikin matsala.

Exit mobile version