An Bizne Robert Mugabe A Kauyen Kutama

An bizne tsohon Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe a mahaifarsa da ke Kutama, makonni uku bayan mutuwarsa.

Mista Mugabe wanda ya mutu yana da shekaru 95, an binne shi ne a harabar gidansu na gado da ke kauyen Kutama a kasar, mai nisan kilomita 90 daga Harare babban birnin kasar.

Mugabe ya mutu a wani asibiti da ke kasar Singapore a ranar 6 ga watan Satumba bayan ya yi fama da doguwar jinya, kusan shekaru biyu kenan bayan hambarar da gwamnatinsa da ya shafe shekaru 37 yana jagoranta.

An dade ana jayayya tsakanin gwamnatin kasar da kuma iyalan Mugabe kan takamaiman wurin da za a binne mamacin.

Sai dai a karshe gwamnatin kasar ta bayar da kai bori ya hau inda ta amince da ra’ayin iyalan Mugabe na binne shi a mahaifarsa da ke Kutama.

Ministocin kasar dai sun so a binne marigayin ne a makabartar da ake binne ‘yan mazan jiya da ke birnin Harare.

Hakan ya sa iyalan Mugabe suka dage kan cewa lallai marigayin ya bar musu wasiya kan cewa a binne shi kusa da mahaifiyarsa mai suna Bona.

Rahotanni sun shaida cewa babu wani mai rike da babban mukami a kasar da ya hallarci jana’izar Mugabe da aka yi a kauyen Kutama kafin binne shi a ranar Asabar, an kuma bayyana cewa daruruwan jama’a ne masu jimami suka hallarci binne tsohon shugaban.

Kafin jana’izar da aka yi wa mamacin a kauyen Kutama, an shirya wata jana’izar a ranar 14 ga watan Satumba a babban filin wasa na birnin Harare inda aka samu halartar shugabannin kasashe da manyan mutane daga fadin duniya.

Misis Grace wato matar Mista Mugabe da kuma yaranshi sun raka akwatin gawar wanda aka rufe shi da tuta mai launin tsanwa da dorowa da ja da baki.

Exit mobile version