An Bude Bikin Yin Sayayya Ta Yanar Gizo Na Kasar Sin

Daga CRI Hausa

Yayin da ranar yin sayayya ta yanar gizo ta kasar Sin wato ranar 18 ga watan Yuni ke karatowa, dandalolin sayar da kayayyaki ta yanar gizo da dama a kasar Sin kamar TMALL, da JD, da Suning da sauransu, sun fara shirya sayar da hajojinsu ga masu bukata.

Masana a wannan fanni suna ganin cewa, bunkasuwar kayayyaki kirar Sin da kuma sayayya a duniya ba tare da barin gida ba, na iya zama sabbin hanyoyin yin sayayya ta yanar gizo a kasar Sin.

A halin yanzu, Sin ta riga ta kasance kasuwa mafi samun kyakkyawar makoma a duniya. Alkaluman kididdigar ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin na nuna cewa, yawan kudaden da aka samu daga sayayyan kayayyaki ta yanar gizo a kasar Sin daga watan Janairu zuwa Afrilun bana, ya karu da kasi 23.1 cikin dari bisa makamancin lokacin bara. Masana sun yi nuni da cewa, bunkasuwar sha’anin yin sayayya ta yanar gizo ta shaida cewa, an kara samun bunkasuwar sabbin hanyoyin yin sayayya yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, abin da ke nuna alkiblar bunkasa tattalin arziki ta hanyar fasahohin zamani. (Zainab)

Exit mobile version