Abdullahi Sheme" />

An Bude Gidan Marayu A karamar Hukumar Funtuwa

A ranar Juma’ar da ta gabata ne a ka bude gidan marayu a garin Funtuwa ta jihar Katsina; gidan marayun, wanda matar Mataimakin Gwamnan Jihar, Hajiya Mariya Mannir Yakubu, ta gina kuma ta bude a unguwar Dandaji a cikin garin Funtuwa.

Bude irin wadannan gidajen marayu kudiri ne irin na wannan gwamnatin da kuma irin jajircewar uwar gidan Mataimakin Gwamnan wajen taimakon marayu.
Tun farko a nashi jawabin shugaban kungiya k. S. na shiyyar Funtuwa, Alhaji Nura Musa Mailemu, ya yaba wa matar Mataimakin Gwamnan wajen kokarinta da hangen nesa da ta nuna wajen ciyar da marayun Jihar gaba da kuma tallaba ma marayu, Shugaban kungiyar k. S. na Funtuwa ya ce, matar Mataimakin Gwamnan ce ta gina wannan gidan kuma ta sanya gadaje da katifu da sauran kayan more rayuwa da kayan amfanin dafa abinci da kuma kayan abinci wanda za a rika dafa abinci, domin taimakon marayun  da kuma samar ma su ingantaccen ilimi, Alhaji Nura, ya cigaba da bayyana irin nasarorin da Hajiya Mariya ke samu a ko da yaushe sun hada da ziyartar gidajen yari, don taimakon su wajen biyan basussuka da akebin wadanda aka yankema hukuncin a gidan yari na bashin da ake binsu da asibitoci don tallabama marasa lafiya, Shugaban kungiya yace babu shakka Hajiya Mariya tana da hangen nesa da son taimako a ko da yaushe yace ta horeni kada a gayyato jama’a wajen kaddamar da wannan abin Alheri tanaso ta zo a sirrance ta bude wannan gidan, amma malaman addini suka umurceni da akira taron Jama’a saboda akwai aiyukan Alheri da ake bayyanawa saboda anaso wadansu bayin Allah na kirki suyi koyi domin aci gaba da taimakon marayu wadanda su ka rasa iyayensu.
Alhaji Nura mai lemu yace yana kara kira ga jama’a da suci gaba da yin addi’oi domin samun zaman lafiya da kawo karshen cutar da ke damun Al’ummar duniya da kasarmu tare da jihar katsina da karaar hukumar Funtuwa.
A nashi Jawabin Shugaban riko na karamar hukumar Funtuwa Alhaji T. Mustapha Kankara ya Godema  matar mataimakin Gwamnan Jihar Hajiya Mariya Mannir Yakubu wajen aikata abubuwan Alheri a fadin Jihar da wanda ta kawo a karamar hukumar Funtuwa yana kira da sauran matan Shuwagabanni suyi koyi da Hajiya Mariya wajen taimakon al’umma baki daya a jihar da kuma nuna son marayu da marasa karfi.
Shugaban riko na karamar hukumar yace babu shakka Gwamnatin karamar zata taimaki wannan gidan marayu kuma karamar hukuma zata ci gaba da ingantashi da abubuwan da jama’ar karamar hukumar ke so.
Daga karshe ya godema Gwamnatin jihar a karskashin Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari wajen kudurinshi na ciyar da jahar gaba da sauran manyan aiyukan da Gwamnatin keyi a halin yanzu a fadin jihar.
A nashi jawabin malamin addinin musulunci Malam Aminu Liman Funtuwa nasiha yayi a kan taimakon marayu da kyautata masu a addinin musulinci. Taimakon marayu ya wajaba a kan kowanne musulmi ba wai sai shuwagabanni ba domin akwai alfanu sosai ga duk wanda ya taimaki marayu, malam Aminu yace bai taba ganin Gwamnatin da da ke kula da marayu ba irin wannan Gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari musamman ma matar mataimakin Gwamna Hajiya Mariya Mannir Yakubu wadda aikinta kenan a koda yaushe na taimakon Al’umma daga karshe ya roki Allah yaba Alhaji Mannir Yakubu kujerar Gwamna idan mai girma Gwamnanmu Aminu Bello Masari ya gama a 2023 Saboda irin natsuwarshi da biyayya da yake da shi kuma na tabbata zai kara kawo gagarumin ci gaba a fadin jihar.
A nata jawabin Shugabar kungiyar k.S network ta jihar katsina kuma uwargidan mataimakin Gwamna Hajiya Mariya Mannir yakubu tayi dogon jawabi a wajen kudurinta da na Gwamnatin jihar wajen inganta rayuwar marayun jihar da marasa karfi. Tace abu ne wanda ya wajaba a gareta tace tuni ta ga amfanin taimakon marayu domin tunda tayi aure bata dade da yin aure ba ta ci gaba da taimakon marayu da marasa karfi, don haka take kira ga dukkan musulmai da su daure suci gaba da taimakon marayu dai dai karfinsu kuma ko yaya domin duk wanda ya taimaki maraya watarana nashi za’a taimaka tunda babu wanda zai dauwwama a duniya kaga wata rana yaranmu marayu ne.
Hajiya Mariya ta inganta gidan marayun kuma ta sanya kayan more rayuwa kamar irin su gadaje da katifu da fankoki da kayan abinci da na dafa abincin irin na zamani da kayan aikin gida wannan shine karo na farko da yankin Futuwa mai kananan hukumomi 11 a aka sami gidan marayu tun lokacin da aka kirkiro da karamar hukumar mulki ta Funtuwa kimanin shekaru 45 da su ka wuce, Hajiya Mariya tace Gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin mai girma Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari zata gina gidajen Marayu a yankin Daura da Funtuwa kuma za’a kara inganta wanda ake da shi a hedikwatar jihar.
Taron ya yi kyau kuma dubban Jama’a ne suka halarci taron inda suka nuna jin dadinsu da  nuna godiyarsu ga Matar Mataimakin Gwamnan Hajiya Mariya Mannir Yakubu.

Exit mobile version