Connect with us

LABARAI

An Bude Kasuwar A Mahuta Baya An Kulle Saboda Cutar Korona

Published

on

An bude sabuwar kasuwa a Mahuta dake cikin karamar hukumar dandume ta jihar Katsina.
Sabuwar Kasuwa mai ci sau biyu a sati a ranakun Talata da Juma’a, babbar Kasuwa ce inda aka tanadi wuraren masu saida abubuwan bukatu ga Al’umma.
Wakilinmu ya zagaya cikin kasuwar inda ya zanta da Shugabannin kasuwar da kuma wasu daga cikin Mutanen da suka zo cin kasuwar daga wurare daban daban.
A nashi jawabin, Sarkin kasuwar Alhaji Amadu K.K ya ce, wannan kasuwar lamarinta daga Allah ne domin yadda kasuwar ke cika da masu saye da sayarwa abin daga Allah ne kuma akwai layi-layi da yawa a kasuwar yace akwai layin masu saida Hatsi da layin masu saida Shinkafa, akwai turakun saida kananan Dabbobi irin su Awaki, da tumaki sannan akwai karar Shanu , da sauran wuraren saida kayan masarufi.
Alhaji Amadu K.K ya ce, a gaskiya suna mika godiyarsu ga Shugaban riko na karamar hukumar dandume Alhaji Ahmed Idris Mashi ganin yadda ya assasa wannan kasuwa kuma ya inganta ta kuma al’ummar yankin masarautar Mahuta suna godiya, ya ce, yana kira ga kantoman karamar hukumar da ya samar masu da kwalbatoci kamar guda biyar a kasuwar kuma a gina masu mayanka dabbobi da samar masu da famfon tuka tuka kamar guda uku da samar da hanyoyin mota da kara sayen filin Kasuwar ganin yadda take cika a ranakun da kasuwar ke ci saboda filin Kasuwar yayi kadan sosai.
Alhaji Amadu K.K ya ci gaba da cewar ya kamata Shugaban riko na karamar hukumar Dandume Alhaji Idris Ahmed Mashi ya taimakesu ya maida dakin ajiye amfanin gona watau Store zuwa bayan Kasuwar ba kamar yadda tun farko aka bada domin suna cikin tsakiyar kasuwar.
A nashi jawabin Shugaban yan kasuwa na kasuwar Mahuta Alhaji Bello yace kasuwar Mahuta kasuwa ce babba kuma Allah ya kafata kuma nanda watanni kadan za ta yi gogayya da sauran kasuwannin kasar nan domin kasuwar na kusa da babbar hanyar Birnin Gwari ta wuce zuwa Lagos sannan ga kayan amfanin gona da ake kawowa daga kowanne lungu na yankin Funtuwa da kuma Shinkafa mai kyau kowa yasan karamar hukumar Dandume wajen noman Shinkafa da sauran kayan amfanin gona manyan dabbobi da sauran kayan masarufi da kasuwar ke samarwa.
A nasu jawaban daban daban, Sarkin Zango Alhaji Bala Buda da Sarkin Fawa Alhaji Babangida Lawal sunyi kira ga masu sayen dabbobi da su ci gaba da zuwa kasuwar Mahuta wajen sayen manyan dabbobi da kanana domin Kasuwar Sabuwa ce kuma ana kawo dabbobi manya kuma kosassu.
A jawabin shi na godiya shugaban yan kasuwa na karamar hukumar Dandume Alhaji K.K godiya yayi ga mai girma Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yadda yake taimakon karamar Hukumar su a ko da yaushe da kuma godiya ga kantoman karamar hukumar akan yadda ya assasa kasuwar kuma zai gudanar da sauran gine gine a Kasuwar.
Alhaji K.K ya gode ma Shugaban yan kasuwa na jihar Katsina da na shiyyar Funtuwa da kuma Kamfanin NAK.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: