CRI Hausa" />

An Bude Sabon Babi Wajen Raya Dangantakar Dake Tsakanin Sin Da Nepal

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gama ziyararsa ta kwanaki 2 a kasar Nepal a jiya, hakan ya bude sabon babi wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Nepal.
Na farko, an tsaida sabon matsayi na aikin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Nepal. Ta hanyar wannan ziyara, an inganta dangantakar abokantaka da yin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, wannan ya shaida cewa, za a samu kyakkyawar makomar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, wato za su samu ci gaba da wadata a nan gaba.
Na biyu, manufar hada kan kasa da kasa ta hanyar hade hanyoyin mota da jiragen kasa da kasar Nepal ta tsara ta hada da shawarar “ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatar, wadanda za su taimakawa kasar Nepal wajen cimma burin samun wadata da amfanawa jama’ar kasar.
Na karshe kuma, Sin da Nepal za su kara yin imani da juna a fannin siyasa. Wato kasashen biyu za su ci gaba da nuna goyon baya ga batutuwan dake shafar babbar moriyarsu, hakan zai taimakawa musu wajen yin hadin gwiwar aiwatar da manufofin samun ci gaba, da more fasahohin samun bunkasuwa, da kuma kara yin hadin gwiwarsu a dukkan fannoni.

(Mai Fassara: Zainab)

Exit mobile version