An Bude Taron Koli Tsakanin Shugabannin Jam’iyyar JKS Da Jam’Iyyun Kasa Da Kasa

Daga CRI Hausa

Da daren yau Talata 6 ga watan nan ne aka bude taron koli tsakanin shugabannin jam’iyyar JKS da jam’iyyun kasa da kasa ta kafar bidiyo. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taro tare da ba da jawabi daga birnin Beijing.

Wannan dai wani muhimmin aikin diplomaisyya ne da Sin take yi, a daidai lokacin da JKS ke cika shekaru 100 da kafuwa.

Shugabannin jam’iyyu da kungiyoyin siyasa fiye da 500, da kuma wakilan jam’iyyu daban-daban fiye da dubu 10 daga kasashe fiye da 160, sun halarci taron, wanda aka yiwa lakabi da “Kawowa jama’a alheri: Nauyi ne dake wuyan duk wata jam’iyya”. (Amina Xu)

Exit mobile version