CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

An Bukaci Al’ummar Sin Da Su Yi Bikin Bazara A Wuraren Da Suke Aiki

by CRI Hausa
February 1, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
3 min read
An Bukaci Al’ummar Sin Da Su Yi Bikin Bazara A Wuraren Da Suke Aiki
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga ranar 28 ga watan Janairu na bana, Sinawa suka fara tafiye tafiyen bikin bazara dake tafe, amma, a bana, al’ummar Sin da yawa sun fi son yin bikin bazara a wurin da suke aiki, domin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

A wannan bikin bazarar da zai sha bamban da yadda aka yi a baya, sassan kasar Sin sun fitar da manufofi da dama domin taya wadanda za su yi biki a wurin da suke aiki murnar bikin bazara.
Hu Fei yana aiki a kamfanin abinci na Jiahe dake birnin Suzhou na kasar Sin, a bana, ya ce, ba zai koma garinsa domin haduwa da iyalansa a bikin bazara ba, shi ya sa, ya aikawa iyalansa kyautuka da dama, domin taya su murnar bikin bazara. Yana mai cewa, “Na saya musu abubuwa da yawa, kamar babbar motar wasa da na sayawa dana, ina fatan zai ji dadi a duk tsawon sabuwar shekara, da kuma samun zaman lafiya.”
Mutane kamar Hu Fei wadanda suka zabi yin bikin bazara a wurin da suke aiki, a maimakon koma garuruwansu, domin ba da gudummawar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, sun cancanci girmamawar jama’a, a sa’i daya kuma, suna samun kulawa sosai daga kamfanoninsu da gwamnatocin sassan kasar Sin.
A sassan kasar Sin da suka hada da lardin Jiangsu, da lardin Zhejiang, da lardin Fujian da dai sauransu, an fidda manufofi da dama, inda aka samar da kyautar kudi ko kudin alawus ga wadanda ba za su koma garuruwansu ba yayin bikin bazara. Sa’an nan, kamfanoni a sassan kasar Sin sun kuma fidda manufar kara tallafi ga ma’aikatansu.
Kamfanin saka na Jinchen dake lardin Jiangsu na kasar Sin ya gabatar da matakai da dama, domin sa kaimi ga ma’aikatan da ba ‘yan lardin Jiangsu ba ne, da su yi bikin bazara a wannan wuri. Kuma matakan da kamfanin ya tsara sun hada da, samar musu da kudin bikin bazara, da kudin gata, da lokacin hutu bayan annoba tare da samun albashi da dai sauransu. Manajan kamfanin Tao Xuejun ya bayyana cewa, “A halin yanzu, galibin ma’aikatan kamfaninmu sun riga sun yi rajistar yin bikin bazara a kamfanin, kuma shugabannin kamfaninmu suna shirya liyafar cin abincin dare a jajibirin sabuwar shekara tare da ma’aikatan kamfaninmu. A yayin liyafar, shugabannin za su taya iyalan ma’aikatan kamfaninmu murnar bikin bazara ta kafar bidiyo, domin mai da wannan bikin bazara a matsayin bikin bazara na musamman ga dukkanin ma’aikatanmu.”
Sakatariyar unguwar Nanyuegong ta birnin Yiyang na lardin Hunan Chen Runzhen ta bayyana cewa, an shirya liyafar cin abincin dare a jajibirin sabuwar shekara ga tsofaffi dake unguwar, wadanda yaransu ba za su dawo garin ba a lokacin bikin bazara, ta yadda, za a kwantar da hankulan yaransu a yayin da za su shafe bikin bazara a waje. Haka kuma, za su kai abinci gidajen tsofaffin, ta yadda za su ji dadin bikin bazaran. Ta ce, “A shekarar da ta gabata, an gyyaci masu dafa abinci zuwa unguwarmu, domin su dafa abinci kala biyar ga tsofaffin unguwar, da nufin samun wadata, wannan ita ce al’adar gargajiyar garinmu. A bana, za a kai karin abinci tsofaffin unguwarmu, domin wasu daga cikinsu sun kai shekaru sama da 90, kuma yaran wasu daga tsofaffin ba za su dawo garin ba a bana, kana wasu tsofaffin ba su da kudin shiga ko yara.”
Bugu da kari, domin magance taruwar mutane, wasu dakin cin abinci sun gabatar da shirin tura masu dafa abinci zuwa gidaje, domin su dafa musu abinci irin garuruwansu. Wani mai aikin dafa abinci a dakin cin abincin Nanjing Lu Qi ya bayyana cewa, sun tsara wani cikakken shirin samar da abinci domin liyafar cin abincin dare a jajibirin sabuwar shekara mai kyau ga al’umma.
Ban da abinci, an kuma tsara wasu shirye-shiryen al’adu ta yanar gizo a sassan kasar Sin, domin nishadantar da jama’a a sassa daban daban na kasar Sin a yayin hutun bikin bazara. Mataimakin shugaban hukumar harkokin yawon shakatawa da al’adu ta birnin Guangzhou na lardin Guangdong Wu Qingsong ya bayyana cewa, “Hukumar ta tsara wasu aikace-aikacen al’adu da yawon shakatawa ta yanar gizo ga mutanen da za su yi bikin bazara a birnin Guangzhou, kamar kallon shirye-shiryen TV, da kallon bikin nune-nune, da kuma yawon shakatawa ta yanar gizo da sauransu. Muna fatan dukkanin al’ummomi dake birnin Guangzhou za su ji dadin bikin bazara.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Ake Yi Wa Jama’a Alluran Riga Kafin COVID-19 Ya Nuna Aminci Da Nagartar Alluran Kasar Sin

Next Post

Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Kare Hakkokin Jama’a A Bangaren Masakun Jihar

RelatedPosts

Muradun Raya Kasar Sin Sun Baiwa Duniya Tabbacin Bunkasuwa

Muradun Raya Kasar Sin Sun Baiwa Duniya Tabbacin Bunkasuwa

by CRI Hausa
36 mins ago
0

Daga CRI Hausa A yau Juma’a ne aka bude taron...

An Gudanar Da Taruka Biyu Na Bana A Wani Muhimmin Lokaci

An Gudanar Da Taruka Biyu Na Bana A Wani Muhimmin Lokaci

by CRI Hausa
41 mins ago
0

Daga CRI Hausa A wannan shekara ce, Jam’iyyar Kwaminis ta...

Li Keqiang: Karuwar GDPn Sin Zai Iya Zarce Kashi 6% a 2021

Li Keqiang: Karuwar GDPn Sin Zai Iya Zarce Kashi 6% a 2021

by CRI Hausa
45 mins ago
0

Daga CRI Hausa Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar...

Next Post
Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Kare Hakkokin Jama’a A Bangaren Masakun Jihar

Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Kare Hakkokin Jama’a A Bangaren Masakun Jihar

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version