Connect with us

LABARAI

An Bukaci Direbobi Su Lura Da Dokokin Hanya

Published

on

Bayani ya fito a kan bukatar direbobi musamman masu safara mutane da dabbobi a tsakani Arewaci da Kudancin kasar nan dasu tabbatar da sun bi dukkan dokokin hanyar a yayin zirga-zirgansu, wannan bayani ya fito ne daga bakin wani ma’aikaci a babban tashar mota ta Isheri a kusa da Bega ta jihar Ogun, mai suna Alhaji Ibrahim Dumbol Yobe, wannada dan asalin karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe, ya kuma yi bayanin ne a yayin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a ofishinsu, ya kuma kara da cewa, wannan kiran ya zama dole ne saboda ganin yadda al’ummar Arewa dake zaune a jihar Legas suke hawa mota domin zuwa gida gudanar da bukuwan sallah da za a gudanar gobe Talata in Allah Ya kai mu.
Daga nan ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya dana jihohi dasu gaggauta gyara hanyoyin kasar nan musamman hanyoyi da suka ratsa zuwa Kudancin kasar daga Arewa, saboda tsananin mahimamcinsu, ya ce, rashin kyawun hanyar yana haddasa hatsarru tare da asarar rayuka da dukiyoyi na dimbin miliyoyi.
Ya kuma ce a dai dai lokacin da ake zirgazirga, kudaden mota zuwa Arewa ya tashi, a inda ake daukar fasinja daga Legas zuwa Arewacin kasa nan a kan Naira Dubu 9,000 zuwa 10,000.
Daga karshe ya bukaci attajira a kasar nan dasu sanya jari a harkar sifiri don kawo wa jama’a saukin tafiye tafiye.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: