Muhammad Maitela">

An Bukaci Gwamna Buni Ya Gina Masana’antun Sarrafa Tumatir Da Shinkafa

Mukaddashin shugaban karamar hukumar Bade (DPM) a jihar Yobe, Alhaji
Adamu A. Dagona ya bukaci Gwamna Mai Mala Buni ya duba yuwuwar kafa
masana’antun sarrafa tumatir da shinkafa a garin Gashuwa da ke jihar
bisa la’akari da yadda garin ya kasance cibiyar noma tumatir da
shinkafa a jihar kana domin bunkasa tattalin arziki, kudin shiga da
samar wa matasa aikin yi.

Alhaji Dagona ya bayyana hakan a sa’ilin da Gwamna Buni yake dora
harsashen ginin kasuwar zamani a garin na Gashuwa- shalkwatar karamar
hukumar Bade makonin da suka gabata.

Ya ce garin Gashuwa cibiya ce ta noman rani, wadda ta dade tana jan
ragamar akalar noma isashen amfanin gona da ake kai shi a kowane lungu
da sakon kasar nan. Ya kara da cewa, “musamman irin yadda manoman mu
su ka shahara wajen noma shinkafa da tumatir mai yawan gaske, wanda ya
dace ace akwai masana’antu a wannan yanki don bunkasa su.”

Advertisements

Shugaban karamar hukumar, ya kara da sanar da cewa, baya ga wadannan,
yankin ya shahara wajen kamun kifi, noman albasa, karas, tattasai,
alkama, da sauran amfanin gona wadanda ake safarar su zuwa sassan
kasar nan daban-daban.

“Bugu da kari kuma, gina wannan sabuwar kasuwa ta zamani da gwamnatin
jihar Yobe take, a Gashuwa za ta taimaka wajen zaburar da matasan mu
fantsama gadan-gadan ga harkokin kasuwanci daban-daban, wanda hakan
zai rage matsalolin rashin aikin yi da fatara a wannan karamar
hukuma.”

A hannu guda, Alhaji Dagona ya ce ko shakka babu wadannan kyawawan
manufofi na gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni wajen aikin gina sabuwar
kasuwar zamani a garin Gashuwa, zai habaka harkokin ci gaban tattalin
arziki a karamar hukumar da ma a jihar baki daya. Ya ce, saboda yadda
garin yake cike da manyan yan kasuwa, kuma hakan zai kara musu kwarin
gwiwa da karsashi a kasuwancin su.

“Haka kuma, gina wannan sabuwar kasuwa ta zamani, ya zo a lokacin da
ya dace saboda kasuwar da ake da ita garin ta dade shekaru aru-aru
kuma ta yi wa yan kasuwar kadan.”

“A gefe guda kuma, ta hanyar samun cikakken goyon bayan gwamnatin
jihar Yobe hadi da shugabanin bangarori a wannan karamar hukuma ta
Bade, mun yi abin a zo a gani wajen yi wa al’umma ayyukan ci gaba,
wadanda su ka kunshi tona rijiyoyin burtsatse, gyara wasu da dama,
aikin yashe magudanun ruwa tun kafin damina ta shigo, don dakile
matsalar ambaliyar ruwa, da sauran muhimman ayyukan da mu ka aiwatar
ga jama’a.”

A karshe Alhaji Adamu Dagona ya yaba dangane da kyawawan kudurori da
manufofin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ga al’ummar jihar Yobe tare
da kula ta musamman ga jama’ar karamar hukumar Bade, halin dattakon da
ba za su taba mantawa dasu ba, har abada.

Exit mobile version