Daga Muhammad Awwal Umar
An bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kirkiro ma’aikatar kula da wutan lantarki ta HYPPADEC don kulawa da matsalolin rayuwar al’uumar da ke yankin.
Shugaban kwamitin bin dokoki da kasuwanci kuma shugaban kwamitin musamman akan hukumar HYPPADEC a majalisar dokokin Neja, Kwamred Abdullahi Shaba, mai wakiltar kananan hukumomin Mokwa da Edati ne yayi kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.
Kwamred Abdullahi Shaba, ya cigaba da cewar wannan itace hanya mafi sauki ta yadda al’ummomin jahohi shida da ya kunshi jihar Fulato, Kebbi, da Neja, Kwara, Kogi da Binuwai zasu iya samun kulawa ta musamman akan matsalolin ambaliyar ruwa da wasu matsalolin na daban da ke damun su.
Abdullahi Shaba, wanda ya nuna rashin jin dadinsa akan mukamin shugaban hukumar da yace maimakon a baiwa jihar Neja saboda gudunmawar da ta ke baiwa tattalin arzikin Najeriya, da kuma ya kamata a ce Neja na da mambobi biyu ne a hukumar.
Yace saboda Neja ita ke da manyan madatsun da ke samar da wuta guda uku da suka hada da Kainji, Jebba da Shiroro kuma su ne suka fi samun matsalolin wadannan saboda yawan ambaliya da barnar da wadannan manyan madatsun ruwan da ke samar da wutan lantarki.
Kwamred Abdullahi Shaba, ya yabawa shugaban kasa akan yunkurin gwamnan Abubakar Sani Bello, Sakataren gwamnatin jiha, sarakuna da kuma ‘yan majalisun tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a jihar da suka bada gudunmawa wajen ganin abinda aka dade ana nema ya samu kuma ya kara da cewar akwai wasu nasarorin na tafe.