Mazuna garin Gobbiya a karkashin inuwar kungiyar ciyar da ‘yan asalin yankin da ke a cikin karamar hukumar Boggoro da ke a jihar Bauchi, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kammala aikin Dam na Gobbiya wanda aka fara shi tun a shekarar 2016.
Shugaban kungiyar ta ciyar da yankin gaba GDA Mista Bulus D. Gobbiya ne ya yi wannan kiran ga Gwamnatin Tarayya a lokacin da sauran mukarabansa suka kaiwa Manajin Darakta na hukumar kula da Koguna ta UBRBDA Abubakar Halilu Muazu da ke a Yola ziyara a ofishin sa dake a hukumar.
Har ila yau, Shugaban kungiyar ta ciyar da yankin taba GDA Mista Bulus D. Gobbiya, ya kuma jinjinawa dan kwangilar da ya fara aikin na Dam, inda Mista Bulus D. Gobbiya ya yi nuni da cewa, a baya an yaudari al’ummar da ke a yankin na Gobbiya kan cewar dan kwangilar an biya shi amma kuma ya ki biyan wasu mazauna yankin da aka yi amfani da wuraren don yin Dam din kudin su na diyya donn gudanar da aiki.
A cewar Shugaban kungiyar ta ciyar da yankin taba GDA Mista Bulus D. Gobbiya, bayan da aka gudanar da dogon bincike kan maganar, an gano cewar, ba a bashi wasu kudade don biyan diyya ga mutanen da abin ya shafa ba.
Shugaban kungiyar ta ciyar da yankin taba GDA Mista Bulus D. Gobbiya ya kuma bayyana jin dadinsa da kuma gidiya ga tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara wanda a cewar
Shugaba Mista Bulus D. Gobbiya Yakubu Dogara ne hummulhaba’isin asasa aikin na Dan.
Shugaban ya kuma yabawa dan Majalisar Dokokin jihar Musa Wakili Makwada dake wakiltar mazabar Bogoro kan nuna damuwar sa kan aikin, musamman yadda ya dinga bin diddigi kan aikin na Dam.
Bugu da kari, Wakilin kamfanin HSR dake gudanar da kwangilar ta aikin Dam Malam Maiwada Bawa ya shedawa Manajin Darakta na hukumar ta UBRBDA cewar, kamfanin ya yi iya kokarinsa wajen gudanar da aikin, inds ya kara da cewa, aikin ya kai kashi 85 bisa dari, inda kuma aikinnna Dam, ya kai kashi 80 a cikin dari na samar da hanya dul da cewar, kaahi 40 bisa dari kacal, ka biya kamfanin na kudin aikin tun a karon farko.
Ya ce, “Aikin ya kai matakin da muka dakar dashi saboda wasu ma’aikatar hukumar sun shirgawa mutane karya cewar har kudin biyan diyya an biya kamfanin don ya baiwa wadanda aikin ya shafi wuraren su.”
Ya kara da cewa, “ A sabaoda barnar da akayi mana ce, hakan ya aanya muka dakar da aikkn gaba dayan sa, amma tunda a yanzu, alummar an fadakar dasu kan lamarin, zamu ci gaba da bayar da kudade don a ci gaba da gudanar da aikin na Dam.”
A cewar sa, akwai kyakyawar fahimta a tsakanin kamfanin da kuma alummar dake a yankin, inda ya kara da cewa, muna kuma jiran a fara biyan diyyar nan bada jimawa ba.
A nashi martanin, Manajin Darakta na hukumar Abubakar Halilu Muazu, ya gidewa akummar kan yaddda suka nuna halin dattako da da’a kan maganar, inda ya sanar masu da cewa, chanjin da aka samu kan aikin ne ya janyo samun jinkirin na biyan diyyar ga wadanda abin ya shafa.