Connect with us

LABARAI

An Bukaci Karfafa Wa Al’umma Wajen Amfani Da Kalandar Musulunci

Published

on

Gwamnatoci da Sarakuna da Malamai da Kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki a Arewacin kasar nan suna da rawa da za su iya takawa domin nusar da al’umma sanin muhimmancin anfani da kirgen kalandar watannin Hijira na addinin musulunci yake da shi a harkokinsu na yau da kullum. Shugaban cibiyar tarbiyar musulunci ta Annur da aka fi sani da “Annur Institute for Islamic Education”Da keda cibiya a Jihar Kano.Malam Auwalu Abubakar Sulaiman Darma ya bayyana haka da yake zantawa da wakilimmu.

Ya cewadannan bangarori na shugabannin al’umma kowanne zai iya taka rawa wajen ganin ana mu’amala da tsarin kalandar addinin musulunci a kowace irin sabga ta yau da kullum ta al’umma hakan zai taimaka wajen sanya musu kishi da kuma sanin muhimmancin aiki da watannin na hijira.

Malam Auwalu Abubakar Sulaiman ya ce an fara anfani da watan hijirane tun zamanin Khalifa Umar sakamakon korafi daya rika samu  na banbancin watannin shekara  sai yasa aka tsara farkon wata da karshen wata na shekarar musulunci wanda aka farada watan hijira na Manzon Allah da ya yi daga Makka zuwa madina cikin Rabi’ul Auwal.amma dan a daidaita kirgen sai aka soma daga watan Muharram.

Ya cesakamakon daular musulunci ta mamaye Duniya a wancan karni na  Khalifofin Mazon Allah  ana amfani da watan musulunci a kusan ko’ina a duniya sai daga baya da turawa suka fantsama kasashen Duniya daya hada harda na Larabawa da Afirka dan cimma burinsu na siyasa da tattalin arziki sai aka samu koma baya wajen amfani da watannin musulunci a yawancin kasasshen musulmi.

Ya yi nuni da cewa duk da Bature ya shigo kasarnan ya yi kokari ya kashe al’adu da koyarwar musulunci musammam a Arewa baiyi nasara a Kano ba bisa kokari da jajircewar malamai da sarakuna wajen yin aiki da koyarwar addini.Yanzu a Nijeriya ta Arewa Sarakuna suna taka rawa musamman ma fadar mai al’farma Sarkin Musulmi ta wajen sanarda ganin jinjirin wata na kowane wata na musulunci da kuma fadar karewarsa wannan yana taimakawa sosai ba wai kawai saina Ramadan kona Zulhajji ba.

Malam Auwal Abubakar  Sulaiman  ya ceirin rawarda malamai suka taka wajen tilastawa Gwamnati ita tasa a baya lokacin Gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta farko a Kano aka soma gabatarda kalandar Musulunci a hukumance,Ya ce lokacin  shi neakasa sakataren kwamitin fitowar kalandar a wannan lokaci kuma kalandar ta karbu daga fitowarata.Wannan tasa a lokacinda Gwamna Shekarau yazo ya ware ranar farko ta Muharram ta zama hutu kuma aka tabbatar da dokar a Gwamnati tasa kuma dokar  sanyawa duk wata takarda kwanan watan musulunci. Sannan kafafen yada labarai na rediyo da jaridu da talabishin suna kokari wajen raya watannin hijira koyaushe.

Ya cesai dai a wannan kokarin farfado da watannin addinin musulunci ana samun karo da abubuwa Biyu wanda na daya shi nekakarinda kasashen turawa masu mulkin mallaka suke na kawo matsaloli,sai kuma rashin tabbacin kwanakin kalandar musulunci a cikin al’umma yana taimakawa kaucewa yin aiki da kalandar hijira a lokacinda wasu ke kirga watan Ramadan da kwana 7 wasu sai suce kwana 5.

Shugaban cibiyar tarbiyar Musulunci ta Annur Malam Auwalu Abubakar Sulaiman yanzu siyarsar tattalin arzikin Saudiyya da wasu kasashen musulunci tasa sun ajiye tsarin watannin hijira saboda faduwar farashin albarkatun man fetur da suka dogara dashi, saboda yin amfani da watan turawa zai basu damar samun rarar kwanaki masu yawa wajen tafiyarda harkokin bunkasar tattalin arzikinsu hakan zai basu damar alkinta kudadensu shi yasa suka rungumi kirgen watan turawa a halin yanzu a harkokin tafiyarda Gwamnatocin kasashensu.

Ya cea kasarnan tamu malamai masu ilimi zasu iya tsara kalandar musulunci dazai tafi a tsari ayi shekaru 50 ana amfani dashi,amma duk da haka wannan canje-canje na fifita watannin masihiyya akan na hijra  ba wani canji dazai kauda mutane daga tsayuwa akan watanni na gudanar da ibadarsu duk abin da ake canzawa ba zai tasiri akan ibadu ba.

Malam Auwalu ya cewatan kalandar turawa na Masihiyya dana Hijira na musulunci duk sunada amfani a wajen musulmi tunda na turawa yana farawane daga haihuwar annabi Musa na hijira kuma daga hijirar Annabi Muhammadu SAW. Wanda duk musulmi za su iya amfani da su a matsayin kirgen wata.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: