An Bukaci Masoya Su Rika Gwajin Kwayoyin Halitta Kafin Aure

Masoya

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

An nemi masoya dake Shirin aure da su yi gwajin kwayoyin halitta kafin yin aure.

Shugabar kungiyar dake tallafa wa masu fama da lalurar cutar amosanin jini wato (sickle cell ta Sickle Cell Patient Health Promotion Center SCHPC ) da ke Kaduna Hajiya Badiya Inuwa Magaji, ta yi wannan Kira  ne yayin ganawa da manema labarai a Kaduna.

Yayin shirye shiryen ranar da Hukumar Lafiya ta duniya ta ware wato 19 ga Watan Yunin kowace shekara ta rananar tunawa da masu wannan lalura domin wayarwa jama’a Kai kan wannan cuta.

Hajiya Badiya Inuwa Magaji, tabayyana cewa yanzu haka sunshiga Unguwanni da Assibitin Koyarwa na Barau Dikko domin wayar da kan jama’a kan wannan allurar.

Ta shawarci masu niyar aure da su yi gwajin kwayoyin halitta kafin yin aure gudun haihuwar masu wannan allurar.

A karshe ta yaba wa Masallatai da ake gudanar da kaurin Aure a Jihar Kaduna da sai sunga sakamakon wannan gwaji na kwayoyin halitta kafin daurawa ma’aurata aure tare da yabawa Majalisar Dokokin Jihar Kaduna dama Gwamnati bisa sanya dokar gwajin kafin daurawa ma’aurata.

 

Exit mobile version