An Bukaci ‘Yan Nijeriya Da Ke Kasashen Waje Su Zuba Jari A Tattalin Arzikin Kasa

Shugaban Cibayar Ma’aikatan Bankuna na kasa CIBN Dakta Uche Olowu ya bayyana cewar cibiyar ta zage wajen jan ra’ayin yan Nijeriya dake zaune a kasashen waje don zu dinga zuba jarin su a cikin tattalin arzikin Nijeriya. Dakta Uche Olowu ya ce, wannan ya na daya daga cikin shirin da cibiyar take yi don wayar da kai a kan zuba jarin. Shugaban ya bayyana hakan a jawabin sa akan wasu shirye-shirye da Cibiyar ta fito dasu a lokacin liyafar cin abincin dare na karashen karo na 53 a ranar Juma’ar data wuce a jihar Legas. Ya ci gaba da cewa, “ Munci gaba da bayar da tamu gudunmawar, a matsayin mu na masu son aci gaba da kuma mayar da hankali a kana masu ruwa da tsaki. Shugaban ya kara da cewa, a saboda hakan ne muna gudanar da taro ta hanyar raeshen mu dake kasar Amurka don baiwa yan Nijeriya mazauna kasar kwarin gwaiwa don zu dinga zuba jarin su a tattalin arzikin kasar nan, musamman don amfanin yan Nijeriya da kuma Nijeriya. Shugaban na CIBN ya kara da cewa, mahukuntan Cibiyar, a kwanan baya cibiyar ta kirkiro da yin tattaunawa ta tsakiyar shekara da nufin yin dubi a kan matsalolin da fannin banki ke fuskanata yadda za’a magance su da kuma daukar matsayi da za’a taimakawa masu ruwa da tsaki. Shima Gwamnan CBN Godwin Emefiele a jawabin sa a wurin taron ya sanar da cewa, CBN zai tabbatar da cewar tsare-tsaren sad a kuma sauran shirye-shiyen sa zasu taimaka wajen samar da ayyukan yi da ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba da magance hauhawan farashi da samar da daidaiton kudin musaya. Acewar sa, “ ina son inyi amfani da wannan damar a wannan daren don jadda da kokarin da CBN yake yi wajenn daukar matakai don kare Nijeriya daga shigo da kaya daga kasashen waje, musamman don a samar da ayyukan yi a kasar nan a tsakanin matasa da inganta hada-hadar kaudi.

Exit mobile version