Daga Alhussain Suleiman,
Kamar yadda na yi wa masu hulda da ni a jihar Kano dama sauran jihohin kasar nan kyakkyawan tadadin kayan abincin dabbobi tare da magunguna har ma da kayan aikin Gona a shekarar da ta gabata, idan Allah ya so haka abin zai cigaba acikin sabuwar shekaran da muka shiga na 2021 da yardar Allah.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin saye da sayar da abincin Dabbobi da mugungunan su har da kayan aikin gonad a sauran su mai suna HUMANE GLOBAL AGROVET dake kwanar masallaci a unguwar Na’ibawa a Kano, Alhaji Bello Abdulkadir Danhassan alokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Malam Bello Abdulkadir Danhassan ya kara bda cewa wani abu kuma da aka samar shi ne sabon dakin gwaje gwajen cututtukan dabbobi mai zaman kan shi , wanda aka tanadi kwararrun likitoci da masana akan abin day a shafi cututtukan dabbobi, wanda nan gaba kadan ake saran gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai bude da yardarm Allah inji shugaban gidan sayar da abincin na HUMANE.
Alhaji Bello Abdulkadir Danhassan kan haka sai ya yi kira ga gwamnati da ta shigo domin warware matsalar da kamfonin suke fuskanta. Harkokin nomad a kiyo abune mai mai kyau da muhimmanci daya kamata acigaba da wayar da kan al’umma.
Da ya ke tsokaci akan matalolin tsaro day a addabi kasar nan kuwa sai masanin aikin gonan ya na da wuya afita daga matsalar tsaro har bsai an samarwa da matasa aikin yi da kuma sana’oin dogaro da kai. Yan’uwan shi yankasuwa kjuma su sanya tsoron Allah tare da kwatanta gaskiya acikin harkokin sun a kasuwanci, sannan har nila yau su kasance suna yin rangwame a cikin kayan da suke saidawa al’umma musamman akwai masu karamin karfi.