Shugaban shirin IFAD na Jihar Katsina, Alhaji Musa Hassan Malumfashi, ya ce, tsarin makarantar manoma ta zamani da a ka bullo da shi ya na daya daga cikin ingantattun hanyoyin ilimantar da manoma dabarun noma a zamanance.
Musa Malumfashi ya furta hakan ne a wajen shirin bayar da horo na kwana daya wanda aka shirya ma shugabannin shirin IFAD na kananan hukumomi da sauran ma’aikatan hukumar ta IFAD.
Ya ce, daidai lokacin da a tsarin makarantu da ake zama aji domin koyar da dalibai, yake kasancewa a haka, shi wannan tsarin ana koyar da manoman ne dabarun noman cikin gonakin su.
Shugaban shirin IFAD dinna jihar Katsina ya shawarci masu samun horon dasu maida hankali kan abinda ake koyar dasu domin kuwa ana sa ran suma su koyar da sauran manoma a kananan hukumomi.
Shi ma da ya ke gabatar da kasida Dr. Gambo Muhammad ya ja hankalin masu daukar horon da su sa lura akan abinda ake koya mu su.
Haka kuma, a yayin da ya ke gabatar da ta shi makalar Alhaji Umar Lawal Mashi yayi bayanin alakar canjin yanayi da wannan tsarin da aka bullo dashi.
A daya bangaren kuwa, Alhaji Muhammad Zubairu Ganuwa ya koyar da mahalartan yadda za a magance matsalar zaizayar kasa da sauran makamantan matsaloli.
Kazalika, Alhaji Kabir Garba Hamisu da Alhaji Kabir Dodo, sun koyar da masu daukar horon yadda za su hada takin gargajiya.
Alhaji Kabir ya nuna masu karara yadda ake yi, ya kuma bukace su da su koyar da ‘yan uwansu manoma na gida.