An Cafke Dan Tsohon Ministan Nijeriya A Cikin ’Yan Fashi A Abuja

Daga Rabiu Ali Indabawa

An damke dan wani tsohon minista a Nijeriya kan zargin yunkurin fashi da makami a wurin canjin kudi a Abuja. A halin yanzu yana tsare hannun hukuma inda ake cigaba da bincike kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wata majiya ta gano cewa wanda ake zargin dan wani tsohon minista ne daga Jihar Benue.

Wata daga wani mutum da ya nemi a boye sunansa ya ce, “Tsohon dan ministan ya kutsa wurin canjin kudin makon da ya wuce a Abuja dauke da bindiga don ya yi fashin kudi. A cikin motar mahaifinsa ya tafi wurin.

“A yayin da ya ke sata a wurin, daya daga cikin masu aiki a wurin ya kama shi ya yi masa duka kafin ya mika shi hannun ‘yan sanda. Fusatattun matasa sun kuma fasa motar mahaifinsa da ya tafi satar da ita.’

“Binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin, ma’aikacin hukumar gwamnatin tarayya ya saba da rayuwar almubazaranci. “Yan uwansa na ta kai da komowa don ganin sun daidaita da mai canjin kudin don a sako shi. “Ana ta kokarin yin rufa-rufa kada abin ya fito fili.”

A halin yanzu dai rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da sanarwa a game da fashin ba. Amma majiyar ta ce: “da gaske ne an kama shi kan zargin fashi a wurin canjin kudi kuma yana hannun hukuma. “Jami’an mu na masa tambayoyi. Bisa alamu ya san abin da ya aikata kuma babu alamar cewa yana cikin maye.

Exit mobile version