‘Yan bindigan da suka kai farmaki gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Ike Ekweremadu, a jijjifin ranar Talata, a lokacin da Maigidan yake ciki da iyalansa, dayan su ya shiga hannu.
Uche Anichukwu, kakakin Ekweremadun ya siffanta lamarin da yunkurin kashe maigidan na shi.
Cikin wata sanarwa, Anichukwu cewa ya yi, “a cikin sadade ne maharan suka wuce masu tsaron gidan na Ekweremadu, wanda yake a Unguwar Apo, Abuja.
Anichukwu ya ce, maharan ba su yi harbi ba ne saboda gudun ankarar da jami’an tsaron da ke cikin gidan.
Ya ce, sai suka kama dan Ekweremadu din, suka tasa shi ya kai su dakin mahaifin na shi.
“A cikin dakin Sanatan ne aka shiga fafatawa, inda har ta kai ga kama daya daga cikin maharan da suke dauke da muggan makamai da kayan fasa gida komai karfin tsaron sa, inda sauran suka sami sa’an guduwa.”
“Gudan da aka kama ya ki ya bayyana komai a kan harin da kuma ‘yan’uwan na shi, don haka sai aka mika shi ga ‘yan sanda.
“In za a iya tunawa, Sanatan ya ketare rijiya da baya ne a wani yunkurin kashe shi da aka yi a Abuja, ranar 17 ga watan Nuwamba, 2015.
“Duk da cewa, an kai rahoton farmakin da aka kai ma shi na 2015 din, amma dai har yau din nan ba wanda ya sake jin wani abu a kan maganan.”