Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ogun ta cafke wani direban motar bas din makaranta mai shekaru 36 wanda ya yi lalata da wata daliba ‘yar shekara hudu, a Ogijo.
‘Yan sanda sun bayyana cewa, an cafke direban bas din ne mai suna, Humble Michael, a ranar 22 ga Janairu, bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai ofishin ‘yan sanda na Ogijo.
Mahaifiyar yarinyar ta fada wa ‘yan sanda cewa yayin da mijinta ke yi wa ‘yarta wanka ne ya lura tana zubar da jini daga al’aurarta.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa, lokacin da aka tambayi yarinyar, sai ta fada wa iyayenta cewa direban motar makarantarsu ne ya yi ma ta haka a ranar 21 ga watan Janairu, yayin da yake tuka ya zuwa gida daga makaranta.
Wannan, in ji shi, “ya bai wa direban damar yin lalata da yarinyar a wani wuri a kan hanya, kuma ya lalata rayuwar karamar yarinyar.”
Oyeyemi ya bayyana cewa, DPO na reshen yan sanda na Ogijo, CSP Muhammed Sulaiman Baba tare da mutanen sa sun bi wanda ake zargin kuma nan da nan aka cafke shi.
An tattara cewa, an kai yarinyar zuwa babban asibiti inda rahoton likitan ya tabbatar da cewa an yi lalata da ita.
Oyeyemi ya kara da cewa, “A lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yarda da cewa lallai ya aikata laifin.”
A halin da ake ciki yanzu, Kwamishinan ‘yan sanda, Edward Ajogun, yayin da ya bayar da umarnin a tura lamarin zuwa sashin yaki da fataucin mutane da kuma bautar da kananan yara na rundunar CIID don gudanar da bincike, ya yi kira ga iyaye da masu mallakar makarantar da su yi taka tsantsan don hana sake afkuwar irin wadannan abubuwan.