Daga Khalid Idris Doya,
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kame wani Hakimin Kauyen Tundan-Iliya da wasu mutum 10 bisa zargin kasancewa ‘yan fashi da makami a karamar hukumar Mashegu da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar ASP Wasiu Abiodun, ya shaida ta cikin sanarwar da ya fitar a jiya Lahadi a garin Minna, cewa biyo bayan rahoton sirri da ta sashin kwararru da suka samu a ranar 25 ga Disamba, tawagar ‘yan sanda ya kaddamar da samame zuwa maboyan ‘yan bindiga da ‘yan fashi da makami a dajin Tunga-Iliya.
Ya ce: “Tawagar ‘yan sandan sun nufi inda suke zargin ‘yan bindigan na boye inda suka yi musayar wuta, tare da kame mutum sha daya, daga cikinsu mutum biyar sun gamu da raunuka.
“Daga cikin wadanda aka kama bisa zargin fashi da makamin har da Sarkin kauyen Tunga-Iliya da wata mai suna Summaya Bello wacce take nemo bayanai tare da sanar da ‘yan fashin bayanai,” inji shi.
Abiodun, ya kuma kara da cewa ‘yan sanda tunin sun fara zurfafa bincikensu kan lamarin kana da zarar suka kammala za su gurfanar da wadanda suka kama din a gaban kotu domin fuskantar tuhuma daidai da laifukansu.
Ya kara da cewa a ranar 25 ga watan Disamban 2020 sun samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga sun mamaye unguwan Gambo da ke karamar hukumar Rafi inda su ka yi garkuwa da mutum hudu.
Ya shaida cewar an samu ceto mutum daya yayin da a ke cigaba da kokarin ceto sauran.