An Cafke Jami’an EFCC 2 Na Bogi A Legas

Kashe

Daga Mahdi M. Muhammad,

An gabatar da wasu maza biyu da wani Sufeton ‘yan sanda wadanda suka yi basaja a matsayin jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), tare da karbar kudaden jama’a da ba su sani ba, a ranar Alhamis a jihar Legas.

Shugaban shiyya na hukumar a Legas, Ghali Mohammed Ahmed, wanda ya yi magana a madadin Shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa, ya ce, an kama gungun mutanen biyu da jami’in ne a New Horizon Estate, Lekki da ke jihar Lega, a ranar Laraba yayin suke gudanar da wata haramtacciyar harkalla don mika ga kotu.

Ahmed ya ce, “Su ukun, Pascal Ugwu Chijioke, Sodik Ibrahim Adekunle da Edwin Bassey, Sufeton ‘yan sanda, sun nuna kansu a matsayin jami’an hukumar ta EFCC, kuma sun kutsa kai cikin gidan da suka nufa tare da kayan aikin da EFCC ta saba sanya wa da tsaro kamar da na jami’an gaske, da jabun jaket din EFCC da katin shaidar EFCC.

“Amma, duk da haka, sun yi rashin sa’a yayin da hukumar ta yi aiki da wani bayanan sirri, ta cafke su. Abubuwan da aka kwato daga wurinsu sun hada da katunan shaida na EFCC na karya, jaket, da kuma ikirarin Kotun da aka ce sun fito ne daga Kotun Majistare ta Mushin, wata babbar motar daukar kaya ta kayan mallakar wanda ba a sani ba,” in ji shi.

Ya ce, wadanda ake zargin sun yi bayanai masu amfani kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da su a kotu.

Wata majiya, wacce ba ta son a buga sunan sa ta ce, lamarin ya faru ne a cikin gidan da yake zaune, inda ta kara da cewa, “daya daga cikin jami’an na bogi ya yi kokarin tserewa ta hanyar tsalle daga wani bene mai hawa hudu amma ya fada kan shingen lantarki.”

Shaidar karya na umarnin kotu da wadanda ake zargin suka kasance suna yi wa wanda suke son damfara.

Ahmed ya bukaci ‘yan Nijeriya su kasance masu lura da taka tsan-tsan a kowane lokaci. Ya ce, “muna bukatar mu yi taka tsantsan da maganganun wannan gungun masu yaudara, kuma mu kai rahoton duk wani ayyukan da ba su dace ba zuwa ofishin EFCC mafi kusa.”

 

 

Exit mobile version