Connect with us

RAHOTANNI

An Cafke Magidanci Kan Zargin Daure Yaro Tsawon Shekara Biyu A Kebbi

Published

on

A jiya rundunar’yan sandan jihar kebbi ta samu nasarar cafke wani magidanci tare da matansa uku kan zarginsu da azartar da yaronsu ta hanyar daure shi a wurin da suke daure dabbobin su na cikin gidan har tsawon shekaru biyu a unguwar Badariya da ke a cikin karamar hukumar mulki ta Birnin-kebbi a jiya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun rundunar’yan sanda jihar, DSP Nafi’u Abubakar yayin ‘yan jarida suka nemi jin ta bakin rundunar ta wayar tarho inda ya ce ” rundunar ‘yan sanda jihar ta Kebbi ta samu nasarar cafke wani magidanci mai suna Aliyu Badariya tare da matansa uku kan zarginsu da azabtar da yaron abukiyar zamansu da Allah ya yiwa rasuwa  ta hanyar daure shi ga turken dabbobin gidan har tsawon shekaru biyu batare da bashi kulawa ba , inji DSP Nafi’u Abubakar”.

Ya ci gaba da cewar ” a halin yanzu ana Kan binciken Malam Aliyu Badariya, Fatima Aliyu, Aisha Aliyu da kuma Rabi Aliyu domin gano dalilin daure wannan yaron dan shekara goma da haifuwa a duniya mai suna Jibiril Aliyu har tsawon shekaru biyu a turken dabbobin na cikin gidan, inji shi”.

Haka kuma ya kara da cewar ” da zarar rundunar ta yan sanda jihar na Kebbi ta kammala bincike zata gabatar dasu a gaban kotun domin yi musu shari’ar.

Bayan faruwar lamarin wakilin LEADERSHIP Ayau ya samu jin bakin Hakimin bangaren da wannan lamarin ya faru a cikin unguwar Badariya, Hakimi Muhammad Attahiru ya ce “gaskiya ne wannan abin ya faru amma a matsayina na Hakimi bantaba samun wannan labari ba sai a jiya da jami’an ‘yan sanda suka kawo samame a gidan Malam Aliyu Badariya wanda nayi mamaki matuka ga faruwar wannan lamarin a cikin yankin da na ke kula da shi,” in ji Hakimi Muhammad Attahiru”.

Ya ci gaba da cewar ” duk da yake bani mamakin faruwar lamarin saboda Malam Aliyu Badariya baiyi shekara daya da dawowa wannan bangaren da na ke riko na cikin Badariya ba, saboda kaga ba kowane zai iya sanin mike faruwa a gidan shi ba ,inji shi”.

Ya kara da cewar ” akwai sakaci na al’umma musamman makwata da ke da bangon gini daya dashi a cewa basu san da irin wannan lamarin ba har sai da jami’an ‘yan sanda suka samu bayanan sirri kafin jama’ar unguwar Badariya suka san cewa ana azarta da wani yaro ta hanyar daure shi har tsawon shekaru biyu a turken dabbobin na cikin gidan na Malam Aliyu.

Bisa ga haka ne Hakimi Muhammad Attahiru yayi kira ga al’ummar yakin da yake kula dashi da su tabbatar da suna sanya ido ga abubawan da ke faru a cikin gidajen mutane don kariya ga aukuwar irin wannan lamarin a nan gaba.

A Bangaren gwamnatin jihar ta Kebbi kan faruwar lamarin, wakilin namu ya samu zantawa da mai baiwa Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu shawara a kan lamuran ci gaban da jin dadi na mata da kuma kananan yara a jihar, Hajiya Zara’u Wali ta ce ” gwamnatin jihar Kebbi ba zata taba lamuntar irin wadannan matsalolin na faruwa a cikin al’ummar ta ba , inji ta “.

Ta ci gaba da cewar ” Bayan gwamnatin jihar ta samu wannan mumular labari na azabtar da yaro danshekara goma da haihuwa a duniya ta hanyar daure shi a wurin da ake daure dabbobin a cikin gida har tsawon shekaru biyu batare da bashi abinci ba, wannan yayi muni matuka , inji Mai baiwa Gwamna Bagudu shawara Zara’u Wali”.

Yanzu haka yanzu gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ta dauki nauyin kai yaron Asibiti domin kula da lafiyarsa da kuma ba shi abinci maigina jiki har tsawon lokacin da ya samu lafiya.

Haka kuma gwamnatin jihar ta Kebbi ta mika kudurin dokar da zata baiwa kowane karamin yaro kariya da kuma ‘yanci ga zaman rayuwarsa a duniya batare da gallazawa ba ko irin wannan matsala ta azabtar wa a gaban majalisar dokokin ta jihar domin tabbatar da cewa kudurin ya zama doka a jihar ta Kebbi da kuma sauran irin wannan matsalolin da ke iya samuwa a cikin al’umma .

Bugu da kari ta bukaci al’umma su rika sanya ido ga irin wannan matsalolin domin bada bayyanan sirri ga gwamnatin ko ga jami’an tsaro don kariya ga aukuwar irin wadannan matsalolin masu munin da kuma bakinciki a yayin faruwar su.

Daga nan ta ce “gwamnatin jihar zata tabbatar da tabi kadin wannan matsala domin ganin cewa doka tayi aikinta ga duk mutanen da ke da zuciyar aikata irin wannan mumunan aiki,” in ji Zara’u Wali.
Advertisement

labarai