Rundunar ‘yan sandan reshen jihar Yobe a ranar Juma’a ta bayyana cewa, ta cafke wani mai suna Sani Sale, mai facin taya, wanda ake zargi da yi wa yarinya ‘yar shekara 15 fyade da kuma kashe ta a garin Gadaka da ke cikin karamar Hukumar Fika na jihar Yobe.
Kakakin rundunar, ASP Dungus Abdulkarim, ne bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Damaturu.
Ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Fabrairu da misalin karfe 7 na safe, lokacin da Sale, mai shekaru 38 da haihuwa, ya yaudari matashiyar, mai sayar da alale, zuwa gidansa da sunan zai sayi abincin.
Abdulkarim ya ce, Sale ya ci zarafin yarinyar tare da yi ma ta fyade, wanda daga baya aka tsinci gawarta a gidan wanda ake zargin, a ranar 11 ga Fabrairu.
Abdulkarim ya kara da cewa, za a mika karar zuwa CID na jihar, Damaturu, don gudanar da bincike cikin tsanaki da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, batun fyade ya karu a kwanan nan a garin Gadaka.
A ranar 8 ga watan Fabrairu, ‘yan sanda sun kuma kama wani mai suna Faruk Mohammed da ake zargi da yi wa wata tsohuwa mai shekaru 90 fyade a yankin.