Rundunar ‘yan sandar jihar Anambra ta cefke wani mutum bisa zargin sa da damfarar mata, inda yake amfani da Facebaook wajen damfarar mata a kan aiki da kuma aure. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Haruna Mohammed shi ya bayyana hakan a Awka cikin jihar Anambra ranar Asabar. Ya kara da cewa, shi wanda ake zargi yana damfarar mata ne masu amfani da Facebook wajen aure da kuma aiki. Mohammed ya ci gaba da cewa, rundanar ‘yan sanda na musamman ce samu nasarar cafke wanda ake zargi. Ya kuma ce, wanda ake zargi yana amfani da sunaye daban-daban har guda uku wanda suka hada da Eugene Chimeze Ohamadike, Henry Eze da kuma Ifeanyi Obiora, an dai cafke shi ne bayan da aka gano maboyansa da ke jihar Inugu. Ya ce,“yana amfani ne da shafin sada zumunta na Facebook inda yake nuna cewa shi ma’aikacin kamfanin mai da ke Fatakwal ne ko kuma shi babban jami’i ne a hukumar da ke kula da hadararruka ta kasa.“Mata dayawa sun fada tarkon shi ne wajen haduwa da shi domin su aure shi”