An Cafke Matashi Da Lafin Fyade A Jihar Legas

Rundunar ‘yan sandar jihar Legas ta cafke yaran mai otal din Dallankester Hotels, Don-Chime George tare da abokinsa Rasak Oke, bisa laifin yi wa yarinya ‘yar shekara 23 fyade a Lekki Phase 1 cikin jihar. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar CSP Chike Oti shi ya bayyana hakan a cikin bayaninsa na ranar Talata, ya bayyana cewa ana zargin George da kuma Oke da bai wa yarinyar kayan maye, wannan shi ya sa ta fita daga cikin hayyacinta, inda suka kai ta otal sannan suka yi mata fyade. Ya kara da cewa, lokacin da yayan yarinyar ya kai rahoton faruwar lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda, nan take rundunar ‘yan sanda sashin Maroko wanda CSP Isah Abdulmajid yake jagoranta suka isa wajen, inda suka cafke wadanda ake zargi tare da kwace bidiyon yin fyaden wanda suka dauka a wayoyinsu.
Oti ya ce, “Binciken rundunar ‘yan sanda sashin bangaran mata ya nuna cewa Razak Oluwaseun Oke dan shekara 28 da kuma Don-Chima George mai shekaru 25 rayon mai otal din Dallankester Hotels da ke Lekki Phase 1 cikin jihar Legas, su ne suka aikata wannan laifi. “Ana zargin wadannan samari guda biyu da kai yarinyar mai shakara 23, kulob a ranar Asabar 2 ga watan Febrairun shekarar 2019, tare da boyayyiyar muradi a cikin zuciyarsu. Lokacin da suke cikin wannan kulob, sun bai wa wannan budurwa kayan maye a cikin abun sha. Lokacin da suka tabbatar da cewa maganin ya bugar da yarinyar, sai suka yi saurin daukanta zuwa otal din Dallankester Hotels, da ke Lekki Phase 1, mallakar mahaifin Don-Chima George.
“A cikin otal din, sun yi mata fyade. Wannan bai isa ba, inda suka dauki bidiyo lokacin da suke yin lalata da ita. “Lokacin da ta barka daga barcin, ta sami wadanda ake zargin, inda suka musanta sun yi lalata da ita. Ta kira yayanta a waya tare da bayyana mi shi yadda lamarin ya auku. Nan take dan uwan nata ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke Maroko, wanda CSP Isah Abdulmajid yake jagoranta, inda suka zo wajen da lamarin ya faru.
“Da suke caje wadanda ake zargin, DPO ya gano bidiyon fyaden a wayoyinsu, inda ya nuna musu yadda suke yi wa yarinyar fyaden.”
Oti ya kuma kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandar jihar Edgal Imohimi ya bai wa sahin bangaran mata na rundunar umurnin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargin gaban kuliya domin ya zama darasi ga wadanda suke aikata irin wannan mummunar aiki.

Exit mobile version